Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin tushen aiki, da wasu ke yi wa kirari da ko nasara yana tsoronki, hudu ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da hudu ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Jiya kusan duk inda ka zaga a soshiyal midiya, da su gidajen rediyo da talabijin har da jaridu da ke intanet, ba labarin da ya fi jini da daukar hankali kamar ziyarar da Mai Martaba Sanusi na biyu ya kawo mana jihar Kaduna, bayan kusan wata biyar da Ganduje ya cire shi a sarautar sarkin Kano. Kuma tun lokacin ziyararsa ta farko fitarsa ta farko ke nan tasa ta kashin kansa ta aiki da ya kawo wa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai. Sarki Sanusi na biyu ya bayyana farin cikinsa da nadin da gwamna ya masa na mataimakin shugaban hukumar bunkasa zuba jari ta jihar Kaduna, da kuma zama daya daga cikin jiga-jigan jami’ar jihar Kaduna.
  2. Al-umar Fulani, da ta Atyap da ta Hausawa da ke karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna, sun yanke shawarar zama lafiya da juna ba sauran tsangwama da takaddama da zubar da jini.
  3. Gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta dokar hana walwala a karamar hukumar Kauru da ta Zangon Kataf.
  4. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  5. Kungiyar kare hakkin bil’Adama mai suna SERAP a takaice, ta bukaci shugaban kasa Muhamnadu Buhari, ya soke hannun da ya sa a sabuwar dokar nan ta kamfanoni da dangoginsu ta shekarar 2020 da har coci-coci suka yi korafin shedaniyar doka ce don ta yi hannun riga da ci gaban coci, hasali ma doka ce da za ta durkusar da coci, kamar yadda suka yi korafi.
  6. Al’umar Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, ba wuta kusan watansu biyar, ba hanya a garin, gadar da sukan samu su haura ta balle, gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  7. Yanzun karfe hudu da minti goma sha biyar na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 322 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 130
Bauci 36
Abuja 25
Edo 17
Bayelsa 14
Oyo 14
Anambara 13
Kaduna 12
Ondo 11
Abiya 10
Oshun 6
Filato 5
Kwara 5
Kano 4
Ebonyi 3
Sakkwato 2
Barno 1

Jimillar da suka harbu 52,227
Jimillar da suka warke 38,945
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1002

Idan aka debe wadanda suka warke daga wadanda suka harbu, aka kuma debe wadanda suka riga mu gidan gaskiya daga wadanda suka harbu, za mu samu jimillar da suka yi saura suke jinya.
Ga jinga nan na bayar a lissafa a ba ni amsa.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Kamar yadda na yi bayani a rubutuna na jiya, an yi kidinafin dandalina na wasaf wato DANDALIN ISHAQ IDRIS GUIBI. Na bude sabo DANDALIN ISHAQ GUIBI. Ga wadanda ke cikin tsohon da aka yi kidinafin, suke kuma so su shiga sabon, su duba cikin tsohon da kyau za su ga sanarwar da aka bayar cewa duk mai son shiga sabon ga LINK wato kofar da za a bi. Sai a kokarta a fice daga tsohon don yana hannun kidinafas kada su hada da shi su tafi da shi.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply