Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, uku ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da uku ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Tsohon shugaban kasa Jonathan ya jagoranci shugabannin kasashen yammacin Afirka zuwa Bamako ta kasar Mali, har shugabannin suka zanta da sojojin da suka yi juyin mulki, da nuna musu cewa juyin mulki ya zama tsohon ya yi yanzu haka a duniya.
 2. Mujallar Tell ta ba Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum lambar yabon shi ya fi
  kowanne gwamna kwazo a Nijeriya.
 3. Gwamnatin Tarayya na ci gaba da kwaso ‘yan Nijeriya da suka makale a wasu kasashen duniya.
 4. ‘Yan sanda sun gayyaci Obadia Mailafiya ya kai kansa da kansa wajensu gobe litinin don amsa wasu tambayoyi a kan wasu laifuka.
 5. Wata kungiya ta mutanen kudancin jihar Kaduna SOKAPU, ta yi zargin cewa a cikin wata bakwai an rasa al’umomi dari da hudu, da mutum dari hudu a cikin wata bakwai. Sai dai wata mutumiyar Zankuwa na cewa a shekarar dubu biyu da goma sha daya, lokacin zaben Jonathan, a rana daya a Zankuwa kadai, an kashe fiye da mutum dubu biyar ba babba ba yaro, ba tsofaffi cikin yini daya, banda sauran wadanda aka kashe a garuruwa da kauyuka daban-daban na kudancin jihar Kaduna. Ta ce har yau ba a daina kisan ba. Ga Manchok da Kagoro da Mabushi da Fadan Kaje da Samarun Kataf me ya faru da Hausawan wajen a shekarar? Me ya faru da Hausawan Madakiya da Matsirga da Gidan Maga da Kwai a shekarar dubu biyu da goma sha daya da ya zama ba sauran bahaushe a wajen?
 6. Kwantenoni da manyan motoci ke dauka a Legas, na ci gaba da fada wa kan jama’a suna mutuwa. Na baya-bayan nan ya fada kan mutum biyu sun mutu.
 7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata hudu ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi.
 8. Yanzun karfe hudu da minti goma sha biyar na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 601 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 404
Abuja 37
Oyo 19
Ondo 14
Abiya 13
Inugu 13
Kaduna 13
Edo 12
Kano 12
Kwara 11
Ebonyi 10
Nasarawa 7
Ogun 6
Oshun 5
Delta 5
Neja 5
Filato 4
Bayelsa 4
Katsina 3
Ekiti 2
Imo 2

Jimillar da suka harbu 50,905
Jimillar da suka warke 38,767
Jimillar da ke jinya 12,129
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 997

 1. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace saboda gadar da sukan samu su haura ta balle, gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Ga wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba. Ga shi sun fi wata biyar ba wutar lantarki, ga shi sun kwashe shekaru ba hanya.
 2. Talakan Nijeriya na ci gaba da korafin komai ya yi tsada musamman kayan abinci. Shinkafa da garin masara ba sa tabuwa.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ba a yi mako guda ba na yi korafin an yi mun kidinafin rubutu, to jiya an yi mun kidinafin wasaf/whatsAp. Ana kidinafin dinsa na bude sabo. Hatta dandalina na DANDALIN IS’HAQ IDRIS GUIBI an yi kidinafin dinsa dole na bude sabo wato DANDALIN IS’HAQ GUIBI. Wanda ke cikin tsohon da aka yi kidinafin, an sa hanyar da zai bi wato LINK don iya baro can ya tare a sabon dandalin nawa. Sannan sauran dandali da zauruka da nake ciki na iya cire ni, daga bisani su mayar da ni. In ba haka ba, sun daina jin duriyata ke nan musamman rubutun da nakan tura musu duk asubah.

Allah Ya mana katangar karfe da kidinafa ko ma wanne iri ne Amin.

Za a iya leka rubutun yau a Taskar Guibi da ke :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply