Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, biyu ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin anabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyu ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Sabbin alkaluman da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa ta bayar a baya-bayan nan na nuna akwai sabbin harbuwa 340 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Kaduna 63
Abuja 51
Filato 38
Legas 33
Delta 25
Gwambe 21
Adamawa 21
Edo 20
Katsina 17
Akwa Ibom 11
Ekiti 10
Ribas 9
Ondo 5
Ebonyi 4
Kuros Ribas 3
Ogun 3
Sakkwato 2
Imo 2
Nasarawa 2

Jimillar da suka harbu 51,304
Jimillar da suka warke 37,885
Jimillar da ke jinya 12,423
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 996

  • Kaduna ta soma zama lambawan wato shalkwatar kwaronabairos.
  1. Gwamnatin Tarayya ta yunkura don farfado da aikin nan da aka yi watsi da shi, na sanya kamarorin daukar duk abin da jama’a ke yi a ko’ina da zai ci dala miliyan dari hudu da saba’in, duk a kokarin da gwamnati ke yi don rage aikata miyagun lafuka da tabbatar da tsaro.
  2. Kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN ta ce sam ba ta amince da sabuwar dokar kamfanoni da dangoginsu ta 2020 da shugaban kasa ya sa wa hannu kwanan nan ba, saboda doka ce da za ta durkusar da coci. Kungiyar ta ce shedaniyar doka ce kuma ya kamata gwamnati ta san cewa coci waje ne na rokon Allah ba na kasuwanci ba.
  3. Wata mata da ake zargin mijinta ya kulleta a daki har kwana uku a Kano ta riga mu gidan gaskiya. Har ila yau a jihar Sakkwato an gano wani magidanci da iyayensa da iyalansa suka kulle shi a wani gida tsawon shekara goma sha biyar. Karo na biyu ko uku ke nan a jihar Kano, sai daya a jihar Kabbi, da ake ta bankado labarin kulle mutum tsawon shekaru.
  4. Na ga wata sanarwa na karakaina a soshiyal midiya da ke cewa an sakar wa al’umar musulmi da ke jihar Kaduna marar gudanar da sallolin nan biyar a jam’i a masallatansu da suka saba, kafin bullar kwaronabairos a hana su.
  5. Matasan kasar Mali na can suna ta farin ciki da juyin mulkin da sojoji suka yi wa Boubacar Keita, da shirya yi wa wakilan kungiyar ECOWAS da ke shirin zuwa kasar ature.
  6. Karon farko bashin da gwamnatin kasar Birtaniya ta ci ya kai Fam Tiriliyan Biyu. €12Tr na ga an rubuta ina fata na fassara daidai?
  7. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce kwaronabairos ba za ta kai shekara biyu a duniya ba, za ta riga mu gidan gaskiya.
  8. Malaman kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, wata biyar ba wutar lantarki, hanya babu, gadar da sukan samu su haura babu, da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzu, Jaja ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi zai gyara musu gadar. Ga wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Allah Ya kawo mu. Don jiya na ce daya ga wata, yawanci da ba su yarda jiya daya ga wata ba, suke cewa jiya biyu ne don sun ga jinjirin watan da kansu, sun ta kirana ko turo mun sako cewa in canza in rubuta biyu ga wata ne, kamar yadda suka ce, ina cikin wadanda ake fi amincewa da bayaninsu na lissafin wata, bai kamata in wayi gari ina batar da jama’a ko kin fadin gaskiya ba. Ni amsar da na bayar ita ce na bi sanarwar Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na uku ne. Suka ce ai shi ma yana kuskure da son rai. Jama’a ina abin yi? Yau biyu ko uku ga wata?

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2682239665381761&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply