Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, daya ga watan Muharram, sabuwar shekarar Musulunci ta 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhamnad S.A.W. Daidai da ashirin da daya ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Shugaban Kasa Muhamadu Buhari ya yi Allah sadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Mali, da goyon bayan duk matakan da al’umar duniya ke dauka a kai.
  2. Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta yanke huldar diflomasiyya da ta tattalin arziki da kasar Mali saboda juyin mulkin da sojoji suka yi.
  3. Kungiyar tarayyar kasashen Afirka A.U. ta dakatar da kasar Mali daga cikinta, tare da bukatar sojojin da suka yi juyin mulki su hanzarta sakin Boubacar Keita da mukarrabansa da suke tsare da su.
  4. Shugaban Kasa Muhamnadu Buhari ya nada Amokachi a matsayin mai taimaka masa na musamman bangaren wasannin motsa jiki.
  5. Kungiyar lauyoyi da za ta yi babban taronta na bana, ta kuma nada gwamna El-Rufai a matsayin mai jawabi a wajen taron, ta ce ta fasa ko janye nadin da ta yi masa a matsayin mai jawabin, saboda zargin da lauyoyin suka yi masa har suka rattaba hannunwansu a kan ba sa son ya halarci taron, saboda zargin yana take hakkin bil’Adama a kudancin jihar Kaduna. Wai ya yi sakaci an kashe har mutum dari hudu da casa’in da uku. Sai dai gwamna El-Rufai ya ce ya yi mamaki a ce kungiya ta masu ilimi da kima a ce tana sauraron bangare guda, ba ta yin adalcin ta saurari daya bangaren.
  6. Yanzun karfe biyu na dare an tsuge da ruwan sama kamar da bakin kwarya, ga ni zaune ina wannan rubutu, kuma an yi sa’a ba su dauke wuta ba.
  7. Ibrahim Magu ya bukaci kwamitin da ke bincikarsa ya ba shi kwafen korafe-korafen da aka yi a kansa.
  8. Hukumomin soja sun ce an kashe sojoji uku, aka ji wa biyu rauni a wani hari da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai garin Kukawa da ke jihar Barno, sai dai ‘yan kungiyar sun kwashi kashinsu a hannun soja, tare da kashe musu mutum takwas.
  9. A juma’ar nan kungiyar ECOWAS za ta mika wa gwamnatin Nijeriya hatsi tan dubu uku, da dari tara da casa’in da tara a Kano, don agazawa jihohi makwabta da suka shiga wani hali saboda kwaronabairos.
  10. An tuhumi wanda ya yi ribas da mota ya banke Tololope ta riga mu gidan gaskiya da laifin kisan kai, da hada baki don kasheta.
  11. Gwamnatin jihar Sakkwato ta ba da hutun juma’ar nan don shiga sabuwar shekarar musulunci. Da ma Kano da Jigawa sun bayar da wannan hutu.
  12. Wasu dalibai da ke rubuta jarabawar WAEC su bakwai a jihar Gwambe sun harbu da kwaronabairos.
  13. Abinci irin su shinkafa, da masara da sauransu na neman su gagari talakan Nijeriya. Komai ya yi tashin gwauron zabi.
  14. Kwamitin da ya saba raba kudi tsakanin gwamnatin tarayya, da jihohi da kananan hukumomi FAAC ya raba naira biliyan dari shida da saba’in da shida, da miliyan dari hudu da bakwai na watan Yuli. Sabanin naira biliyan dari biyar da arba’in da uku, da miliyan dari bakwai da tamanin da takwas da aka raba a watan Yuni. Gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan dari biyu da saba’in da uku, da miliyan dari da tamanin da tara. Jihohi sun samu naira biliya dari da casa’in da miliyan dari takwas da arba’in da tara. Sai kananan hukumomi da aka ba naira biliyan dari da arba’in da biyu, da miliyan dari bakwai da sittin da daya. Inda a da ne, da an sa ran dilin-dilin a makon gobe.
  15. Naira ta fado a kasuwar hada-hadar kudi saboda karancin da dala ta yi. Dala tana a naira dari hudu da saba’in da bakwai, sai fam a naira dari shida da takwas, sai euro/yuro a naira dari biyar da hamsin.
  16. Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe naira biliyan goma sha uku don kankamar tsarin tsaro da al’uma za ta taimaka da aka fi sani da COMMUNITY POLICING.
  17. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya ce ‘yan bindiga da suka hana kasar nan sakat na da alaka da kasashen ketare.
  18. A kudancin jihar Kaduna wuraren Zangon Kataf da Kajuru an kashe mutum a kalla goma.
  19. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamatin tarayya, har da na jami’o’i, na ci gaba da korafin shekara daya da wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  20. A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe don duba shafukana da ke dauke da rubutun labarun da na kawo muku, daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.
  21. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, wata biyar ba wuta, ga ba hanya, gadar da sukan samu su hauro ta balle, da shugaban karamar hukumar Kudan, Jaja ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi, zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  22. Yanzun karfe hudu na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 476 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 235
Abuja 44
Kaduna 41
Barno 33
Filato 28
Abiya 13
Edo 13
Ribas 12
Imo 11
Oyo 10
Kano 9
Kwara 7
Inugu 5
Katsina 5
Gwambe 4
Ogun 4
Nasarawa 1
Zamfara 1

Jimillar da suka harbu, 50,964
Jimillar da suka warke, 37,569
Jimillar da ke jinya 12,403
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 992

Mu yi juma’a lafiya.

Af! Wani ilimi ne na karu da shi a tashar talabijin ta TVC mai suna GRAPHOCOLOGY. Ina fata na kwafo sunan daidai? Ilimi ne da ake iya gano ko kai wanne irin mutum ne ta hanyar irin rubutunka da biro ko alkalami. Har wasu kasashe kan dauki mutum aiki ko kin daukarsa ta gano halinsa ta rubutun da ya yi ba wai kwazo a jarabawa ko ganawa ba. Rubutunsa kawai da ya yi da biro ya wadatar an gano kirkinsa ko akasi. Ko wajen neman aure ana cewa ya yi rubutu, daga rubutun yadda ya jera su, wara-wara ko matse da juna a kalmomin za a iya gane zai iya cefane ko ba zai iya ba.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

One Thought to “Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi”

  1. […] Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi […]

Leave a Reply