Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, ko dai daya ga watan Almuharram, sabuwar shekarar Musulunci ta 1442, ko kuma talatin ga watan Zuhijja, na shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Gwamnatin jihar Kano ta ba da hutu yau alhamis, domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1442.
- Sojojin da suka yi wa Boubacar Keita na Mali juyin mulki, sun ce za su shirya zabe nan ba da dadewa ba, sun sa dokar hana walwala da rufe kan iyakokin kasar.
- Nijeriya ta rufe ofishin jakadancinta da ke Ottawa a Canada/Kanada.
- Taron Majalisar Zartaswa na jiya ya amince a kashe wata naira biliyan hudu ba wasu mutsamutsai wajen aiki kashi na biyu na Dam din Usama da ke Abuja, da batun gidaje.
- A jihar Taraba, gwamnatin jihar ta bi gida-gida, har gida dubu ashirin da shida, ta tallafa musu da kayan tallafi na kwaronabairos.
- Sojojin sama sun kashe ‘yan bindiga ashirin da tarwatsa tungarsu a jihar Barno, kafin nan ‘yan bindigan sun kai hari Magumeri suka bankawa asibitin da gwamnati ta gyara, da kamfanin sadarwa daya tilo da ke wajen da sauransu wuta. Suna cikin haka sojoji suka musu dirar mikiya.
- Kungiyoyi da hukumomin tashoshin jiragen ruwa na kasar nan ba su yarda da wani yunkuri na kara kudin dakon sunduki/kwantena zuwa kasar nan da kashi dari hudu ba.
- Kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta kammala nata tsarin da ta kira APP a madadin IPPIS da ta ce ba ta yarda da shi ba, don gwamnati ta gwada shi ta gane akwai bambanci da kuma sahihanci ba walawala irin na IPPIS ba.
- Gwamnatin Tarayya za ta kara himma wajen kyautata ayyukan kula da lafiya matakin farko don rage mace-macen mata da jarirai a lokacin nakuda da haihuwa a kasar nan.
- Wata ‘yar ajin karshe a sakandare da ke rubuta jarabawar fita ta WAEC a jihar Kwara ta harbu da kwaronabairos, saboda haka aka kebeta take jarabawarta ita kadai.
- Ana ta korafin ana ganin tambayoyi da amsoshin jarabawar WAEC da dalibai ke kan rubutata ta soshiyal midiya kafin ranar rubuta jarabawar.
- A jihar Neja jami’an tsaro na nan sun dukufa suna farautar wasu ‘yan bindiga da suka kashe wasu sojoji a kalla biyu da wani dan sintiri, suka kuma sace wani bature.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi har yanzun shiru.
- Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Yamacin Afirka ECOWAS, ta dakatar da kasar Mali daga cikinta saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
- Biden ya yi nasarar tsayar da shi a matsayin dan takaran demokrat a zaben shugaban kasa na Amurka da za a yi.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin rabonsu da wutar lantarki sun kai wata biyar, ga ba hanya, ga gadar da shugaban karamar hukumar ta Kudan, Jaja ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, in sun zabe shi zai gyara musu ta karasa ballewa, ga wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Jiya na gama rubutuna tatas, na sake shi da karfe hudu na asubah, na neme shi na rasa. Wasu masu tsokaci suka ce kidinafas ne suka yi awon gaba da shi. Sai na biya. Wasu suka ce ba mamaki ministan labaru ne ya tarbe rubutun. Wasu suka ce ya yi layar zana ne. Ni kuma na ce batar dabo ya yi. Wani ya ce ko dai ana TRACKING rubutun nawa ne? Rubutu dai ya yi nisan kiwo. Har yanzun bai dawo ba.
- Yanzun karfe hudu da minti goma sha biyar na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwarona mutum 593 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Filato 186
Legas 172
Abuja 62
Oyo 27
Delta 25
Ribas 20
Ondo 19
Edo 18
Kaduna 17
Inugu 12
Akwa Ibom 10
Ogun 7
Abiya 6
Gwambe 7
Kano 3
Oshun 3
Jimillar da suka harbu 50,488
Jimillar da suka warke 37,304
Jimillar da ke jinya 12,199
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 985
Mu wayi gari lafiya da shiga sabuwar shekara lafiya.
Af! Ana ta ci gaba da fassara rubutuna zuwa turancin Ingilishi a baibai. Ina dai kara ankarar da jama’a cewa ba ni ke yin wannan fassara ba. Wasu sun ce fesbuk ke karambanin fassarawa. Ko ma dai wane ne ke fassarawa to bai iya fassara ba.
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2680588162213578&id=2356865571252507
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.