Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, ashirin da takwas ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha takwas ga watan Agusta, shekarar dubu biyu da ashirin.

Muhimmiyar Sanarwa
Jiya abokina Lawal Ali Garba ya ankarar da ni cewa wani yana fassara labarun da nake rubuwata zuwa harshen Ingilishi. Ni ban iya ganin fassarar ba, amma ya karanto mun fassarar da aka yi wa rubutuna na shekaranjiya, inda kasssara ake yi ba fassara ba, kuma turancin sai a hankali da ko ni da ban iya turanci ba, na yi fiye da shi. Saboda haka nake rokon mai fassarawa yake kuma raba fassarar da rubutuna ya daina. Kuma duk wata fassara da aka gani ta rubutuna ba ni na yi ta ba.

 1. Oshiomhole ya je fadar shugaban kasa ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan zaben jihar Edo da ke tafe.
 2. Kotu ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri da ba da uarnin gudanar da wani zaben cikin kwana casa’in, sai da gwamnan ya ce zai daukaka kara.
 3. Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa ashirin da tara ga watan nan za a dawo da zirga-zirgar jiragen sama zuwa kasashen waje, da za a fara da tashar Abuja da ta Legas.
 4. Hadin gwiwar kungiyoyin daliban jami’o’in Nijeriya, da kwalejojin foliteknik, da kwalejojin ilimi da sauransu, za su yi zanga-zanga gobe laraba, don tilasta wa gwamnati bude musu makarantunsu don su koma su dora da karatunsu daga inda suka tsaya.
 5. Shugabanin kungiyar kiristocin Nijeriya, sun ziyarci gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai a kan rikicin kudancin jihar Kaduna.
 6. An dawo da wasu ‘yan Nijeriya da suka je aikatau Labanan su wajen dari gida.
 7. Ana can ana ci gaba da cin zarafin ‘yan Nijeriya da ke neman halaliyarsu a kasar Ghana, abin ba ko dadin ji.
 8. Rabon da mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna su ga wutar lantarki sun kai wata biyar, ga gadarsu ta balle, ga hanya ba su da ita, ga makarantarsu ta firamare ko akurkin kaji albarka.
 9. An yi tsiya-tsiya tsakanin ministan sufuri Amaechi da wani kwamiti na majalisar wakilai a kan wani bashi na kasar Caina.
 10. Ma’aikatan mai sun dakatar da yajin aiki a kan albashinsu.
 11. Sojojin sama na Nijeriya, sun ci gaba da luguden wuta ta sama, wuraren da ‘yan kungiyar Boko Haram suka fake a jihar Barno.
 12. Jiya dalibai suka soma rubuta jarabawar WAEC ta kammala sakandare.
 13. Ghali Na’Abba tsohon shugaban majalisar wakilai ya amsa wata gayyata da hukumar tsaro ta DSS ta masa a kan wani tsokaci da aka ce ya yi a kan mulkin Baba Buhari.
 14. Obadia Mailafiya ya kuma kai kansa hukumar DSS da ke Jos don ci gaba da masa tambayoyi a kan kalaman da aka ce yayi cewa akwai wani gwamna da ke jagorantar Boko Haram.
 15. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya, wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi, haka nan wasu malaman jami’o’i a gwamnatin tarayya, wasu na bin albashin wata daya, wasu wata biyu, wasu uku, wasu hudu, wasu biyar, kodayake wasu bayanai na nuna gwamnati ba ta da kudi.

16.Kasar Sin wato Caina, da ake zargin daga can kwaronabairos ta kyankyashe ta buwayi duniya, ta gano maganin cutar, bayan maganin da kasar Rasha ta gano ita ma.

 1. Yanzun karfe hudu da rabi na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 417 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 207
Kaduna 44
Ondo 38
Abiya 28
Anambara 21
Filato 20
Bauci 13
Oyo 9
Ebonyi 9
Delta 7
Edo 7
Inugu 6
Neja 3
Gwambe 2
Ogun 1
Abuja 1
Kano 1

Jimillar da suka harbu 49,485
Jimillar da suka warke 36,834
Jimillar da ke jinya 11,674
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 977

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya Allah Ya yi wa abokiyar aikinmu a gidan talabijin na jihar Kaduna, da ke zaune a titin Gwandu da ke cikin garin Kaduna Hajiya Raliya Sani rasuwa bayan wata jinya. Mun yi aiki da ita a KSTV da Capital TV, ikuma in dai kuna wasaf da ita, to kullum da karfe shida na safe sai ta turo maka sako na fatan alheri ba fashi kamar yadda nake rubutu duk asubah. Har na yi mamaki rabon da ta turo mun tun ranar laraba da ta gabata karfe tara da rabi na safe wato 12/8/2020. Kuma ko a jiya ta hau wasaf da safe kafin ta rasu da rana. Na dawo daga tafiya ina bude fesbuk sai na ga tsohon abokin aikinmu a KSTV Sabo Suleman ya rubuta rasuwar tata.

Ga sakon da ta turo mun ranar ta laraba:

“Wish U Good Health
Happiness And Peace”

Sai wanda ta turo mun talata kafin larabar:

“Let us thank God for a brand new day
Good morning”

Sai wanda ta turo mun litinin kafin talatar:

“Good Relations are those…
Who Care Without Hesitation, Who Remember Without Limitations, & Who Remember the Same Even Without Communication. Beautiful Morning”

Sai wanda ta turo mun lahadi kafin litinin:

“Good Morning
Enjoy Your Sunday”

Kamar yadda na bayyana da farko haka take turawa duk wanda take da lambarsa kuma suke wasaf tare. Ga ta da zumunci don har gidana tana zuwa da motarta in ta tononta ina ce mata Rally Loss tana ce mun Guibi Love.

Allah Ya jikan Hajiya Raliya Sani Ya gafarta mata kurakuranta, mu da muka yi saura, Ya sa mu cika da kyau da imani Amin.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply