Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, ashirin da bakwai ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhamammad S.A.W. Dai-dai da goma sha bakwai ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Hukumomin sojan saman Nijeriya, sun tura dakaru na musaman kudacin jihar Kaduna don tabbatar da zaman lafiya. A wata hira da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ce rikicin kudancin jihar Kaduna ya somo daga Kasuwar Magani wuraren shekarar 1980 zuwa 1981, kuma duk bayan shekara uku ko hudu sai an sake yi a kudancin jihar Kaduna ko daga can ya bazu sauran sassan jihar Kaduna. Gwamnan ya ce a lokacinsa ne rikicin ya daina yaduwa ko bazuwa zuwa wasu sassan jihar Kaduna saboda kokarin da gwamnatinsa ke yi idan irin wannan rikici ya somo daga can.
  2. A jihar Yobe wasu ‘yan bindiga sun sace wani dagacin kauye da dansa a karamar hukumar Fune, sai dai yaron ya samu ya kubuce wa ‘yan bindigan saura mahaifinsa.
  3. A jihar Kaduna, an gano wata budurwa Sadiya da wani mai wa’azin kirista ya sace ta a Tudun Nufawar Kaduna tun shekarar 2013, lokacin tana ‘yar shekara goma sha uku, ya kaita makarantar mishan da ke Jos bayan ya kiristar da ita. Bacewarta ta yi sanadiyar mutuwar mahaifinta da jefa danginta cikin mawuyacin hali. A yanzun an ganota shi kuma da ya saceta da canza mata addini yana hannu.
  4. Wasu matasan Arewa masu kaunar zaman lafiya, sun bukaci a sallami Obadia Mailafiya daga cibiyar nazarin muhimman bukatu ta kasa NIPSS.
  5. A shirye-shiryen zaben jihar Edo da Ondo, shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya umarci kwamishinonin ‘yan sanda su sanya ido a kan wadanda ke rike da makamai.
  6. Jama’a na ci gaba da tambayar inda aka kwana tsakanin ‘yan majalisa da minista Akpabio da ya ce su ne ke aiwatar da yawancin kwangilolin yankin Neja Delta, har suka ba shi wa’adin ya wallafa sunaye. Shiru tsakaninsu ba amo ba labari.
  7. Hukumar Kididdiga ta Kasa ta ce rashin aikin yi ya karu da kashi 27 da ‘yan kai a karshen watanni shida na farkon shekarar nan da muke ciki.
  8. Za a dinga duba farashin mai daga wata zuwa wata, ko farashin ya yi sama ko ya yi kasa, ya danganta ga yadda farashin ya kaya a kowanne wata.
  9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’a na korafin wasunsu na bin albashin wata daya, wasu wata biyu, wasu wata uku, wasu wata hudu.
  10. Yanzun karfe hudu da rabi na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 298 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Filato 108
Kaduna 49
Legas 47
Ogun 18
Oshun 17
Abuja 15
Ondo 14
Edo 8
Oyo 6
Akwa Ibom 4
Kuros Ribas 4
Barno 3
Ekiti 2
Bauci 1
Kano 1
Ribas 1

Jimillar da suka harbu 49,068
Jimillar da suka warke 36,497
Jimillar da ke jinya 11,596
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 975

  1. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace ba shiga ba fita, saboda ballewar gadar da suka saba haurawa, da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa ya kasa gyara musu gadar.

Mu wayi gari lafiya.

Af! A rana mai kamar ta yau 17 ga watan Agusta na shekarar 2018, da karfe hudu da rabi na asubah wato daidai wannan lokaci, yau shekara biyu daidai na yi wannan rubutu kamar haka:

‘Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, shida ga watan Zulhaj, shekara ta 1439 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha bakwai ga watan Agusta, shekara ta 2018.
Ina fara wannan rubutu karfe hudu da minti goma sha biyar na asubah aka soma ruwan sama ga shi nan da karfinsa. Allah Ya sa mu ga wucewarsa lafiya Amin.

Labarin farko ka ji a ‘yan kwanakin nan ko’ina tsit ba satar jama’a, babu garkuwa da jama’a, ba kashe jama’a da ba su ji ba ba su gani ba ko ta da garuruwa. Tsaro ya inganta. To ashe dama wargi wuri ya samu. Kuma na ji ana kokarin sake fasalta tsarin aikin ‘yan sanda a kasar nan ba tare da bata wani lokaci ba.

Sai zaman da kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai, da suka yi jiya don duba kasafin naira biliyan dari da arba’in da uku da Shugaban Kasa ya tura musu don amince wa hukumar zabe ta kasa ta kashe su wajen gudanar da zabubbukan 2019. Kwamitin ya zauna jiya har ya ma nemi shugaban hukumar Farfesa Mahmud ya je gaban kwamitin don karin haske a kan wasu bangarorin kasafin.

Sai hutun Sallah da gwamnatin tarayya ta ba da talata ashirin da daya ga wata, da laraba ashirin da biyu ga wata na Agusta. A koma aiki alhamis ashirin da uku ga wata. Har wasu na sa ran jin dilin-dilin kafin Sallah.

Jiya ma wutar lantarki ba laifi sun bar mana ita.

Mu yini lafiya’

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply