Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, ashirin da shida ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha shida ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Hukumomin sojan Nijeriya sun ce sun kammala bincike a kan zargin da gwamna Zulum ya yi cewa sojojin da aka tura yakar Boko Haram sun tare a Baga suna sana’ar kifi, cewa ba gaskiya ba ne, tare da ba gwamnan shawarar ya dinga bincikar bayanai da kyau a kan sojojin kafin ya kai ga yin zargi mara tushe.
 2. Majalisar Dattawa ta ce za ta lallashi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori manyan hafsoshin tsaron kasar nan tunda sun lura sun kasa tilasta masa ya kore, duk da tsaro na ci gaba da tabarbarewa a kaaar nan.

3.Hukumomin Babban Birnin Tarayya Abuja sun rushe gidaje guda dari da talatin da hudu a al’umar Apo Akpajeriya da hanyoyin mota za su bi, sai dai an ba al’umar wasu wuraren komawa.

 1. Daular Larabawa ta ba Nijeriya gudunmawar kayayyakin jinya masu tarin yawa, da wani babban jirgin sama ya kawo wa Nijeriya jiya da safe.
 2. Wata kotu da ke Abuja ta tabbatarwa da Diri Douye kujerarsa ta gwamnan jihar Bayelsa, bayan watsi da ta yi da wasu korafe-korafe uku a kan zabensa, har da umartar wadanda suka kai kara a kan zaben nasa su biya shi wasu kudade.
 3. Wasu ‘yan gida daya su bakwai da ke jihar Zamfara, sun riga mu gidan gaskiya sakamakon wani abinci da suka ci gurbatacce.
 4. ‘Yan kudancin jihar Kaduna sun yi wata zanga-zanga a ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja.
 5. Ana zargin wani Difi’on ‘yan sanda da aka ce ya yi suna wajen kisa, ya kashe wasu matasa biyu da ake zargin sun saci kaji, ya karairaya daya a jihar Bauci.
 6. A jihar Kabbi an kama wani magidanci da matarsa da laifin daure dan kishiya da suke zargin ba shi da lafiya, cikin garken dabbobi yana komai tare da dabbobin.
 7. A jihar Kano an damke wasu iyaye da suka kulle dansu a daki ya shekara bakwai a kulle a cikin dakin saboda suna zargin yana shaye-shaye.
 8. A jihar Legas an kama mutumin da aka gani a bidiyon da ke ta karakaina yana casa wata ‘yar sanda yelofiba a bainar jama’a.
 9. A jihar Kaduna mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan, na can suna ci gaba da kasancewa a killace ba shiga ba fita, sakamakon ballewar gadar da sukan samu su haura, da shugaban karamar hukumar ta Kudan ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan suka zabe shi zai gyara musu. Ga wa’adinsa na shirin karewa ya kasa gyara musu.
 10. Hukumar kula da gidajen rediyo da talabjin ta kasa NBC ta ce sun yi hannun riga da sauye-sauye ko gyaran da ministan labaru Lai Mohammed ya ce yana kawo musu.
 11. Ma’aikatan foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi har yau shiru. Haka nan wasu malaman jami’a na korafin wasu watansu daya, wasu biyu, wasu uku wasu hudu ba albashi babu dalilinsa.
 12. Yanzun karfe hudu da minti goma na asubah. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 325 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 87
Abuja 49
Gwambe 28
Ebonyi 20
Filato 19
Kwara 18
Inugu 17
Imo 12
Ribas 12
Kaduna 11
Ogun 10
Edo 9
Oyo 9
Ondo 8
Oshun 8
Ekiti 4
Barno 1
Kano 1
Bauci 1
Nasarawa 1

Jimillar da suka harbu 48,770
Jimillar da suka warke 36,290
Jimillar da suke jinya 11,506
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 974

 1. Al’umar Kinkinau da ke karamar hukumar Kaduna ta kudu na korafin suna fama da barayin rana, da ke yawan haurawa gidan da suka san ba kowa da rana. Misali miji da matan sun tafi aiki sun bar gidan ba kowa, sai su haura ta katanga su sace musu talabijin da kwamfuta da kudi, da sauransu. Har ake ba magidanta shawarar in mutum matarsa daya, kuma duk suna fita aiki, to ya daure ya karo wata matar da ba ta zuwa aiki ta dinga kula da gidan.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Na lura da yake nakan fara rubutu karfe biyun dare zuwa karfe hudu ko biyar na asubah, akwai wani zakaran makwabta da ke soma cara da karfe ukun dare, can sai zakarun gidana ka ji suna kada fikafikai suna amsawa. Haka ma da karfe hudu ko hudu da minti biyar. Har zuwa biyar da kusan rabi da ake tayar da Sallar asubah. Da karfe uku na rana sai na kasa kunnena in ji ko zakarun za su yi cara? Ilai kuwa sai na ga sun fara. Abin da nake kokarin ganowa shi ne, karfe nawa zakaru ke cara? Dole sai da asubah suke yi ko har da rana? In har da rana suna yi to daidai karfe nawa? Me suke yi kafin su fara cara? Me ya sa daidai karfe ukun suke soma cara? Baiwa ce ko koyo suke yi? In koyo ne wa ke koya musu? In baiwa ce ta ya suke samun wannan baiwa, ana haihuwarsu da ita ne ko sai sun girma sun balaga baiwar ke zuwa musu? Wanne nau’in zakari ya fi iya cara da murya? Akwai bambancin shekaru a iya carar? In zakara ya kai wasu shekara yakan daina cara? Me ya sa kaza ba ta yin cara? Me ya sa kaza ke gudun famfalaki idan zakara na so ya mata barbara? Da gaske zakara na yin kwai?

Za a iya leka rubutun nawa na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=514633779338939&id=114506719351649

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply