Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, ashirin da biyar ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha biyar ga watan Agusta, shekarar dubu biyu da ashirin.
- Gwamnatin Tarayya ta yi nuni da cewa Nijeriya fa ta hau wani siratsi/siradi na rashin kudi da in aka yi wasa albashi ma zai gagareta biya.
- Ministan lafiya Mamora ya bayyana damuwarsa a kan yadda ma’aikatan lafiya ke ta harbuwa da kwaronabairos babu kakkautawa a kasar nan.
- Hukumar Kula da Al’amuran Masu Shari’a ta Kasa NJC a takaice, ta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar ya nada alkalan kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa, su zama alkalai a kotun koli. Alkalan su ne mai shari’a Abu Aboki, da Mohammed Garba, da Tijjani Abubakar, da Mohammed Saulawa.
- Sojojin Sama na Nijeriya sun kai farmaki wurare daban-daban na kungiyar ISWAP da Boko Haram da ke jihar Barno, suka kashe da dama da musu barna.
- Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani dan majalisar dokoki a jihar Bauci, suka tafi da matansa biyu da diya.
- A jibi litinin goma sha bakwai ga watan nan ‘yan ajin karshe na karamar sakandare wato JSS 3 za su koma makaranta.
- An bude kasuwanni na jihar Kaduna bayan watanni da suka kwashe a kulle. A nan cikin garin Kaduna, ‘yan kasuwa da dama sun ce hajarsu ta miiyoyin naira ta lalace a rumfunansu saboda ba saye da sayarwa, duk kayan sun lalace.
- Ma’aikatan mai sun yi zanga-zanga tare da barazanar zuwa yajin aiki a kan kin biyansu albashi.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata biyar ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi. Haka nan wasu malaman jami’a na bin albashin wata daya, wasu wata biyu, wasu wata uku, wasu wata hudu wasu wata biyar. Kodayake ita kanta gwamnati ta ce ta yi BUROK. Da ke nuna a ma gode har ana iya ma biyan wasu ma’aikatan albashin.
- Yanzun karfe hudu da rabi na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 329 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Lagos 113
Kaduna 49
Abuja 33
Filato 24
Kano 16
Edo 15
Ogun 14
Delta 13
Oshun 10
Oyo 8
Ekiti 6
Bayelsa 6
Akwa Ibom 5
Barno 4
Inugu 4
Ebonyi 3
Ribas 2
Bauci 1
Nasarawa 1
Gwambe 1
Neja 1
Jimillar da suka harbu 48,445
Jimillar da suka warke 35,998
Jimillar da ke jinya 11,474
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 973
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, ba shiga ba fita saboda karyewar gadar da suka saba bi su haura, da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzu, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, cewa idan suka zabe shi zai gyara musu gadar. Sun zabe shi, ga wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu gadar ba.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Wani ke tambayata mene ne burina? To babban burina kada in zama dan siyasa.
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2676462159292845&id=2356865571252507
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.