Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, goma sha tara ga watan Zulkida, shekara ta 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha daya ga watan Yulin shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Da fatan yau za a mun hakuri labarun ba yawa saboda matsalar wutar lantarki. Haka muke yini mu kwana babu wutar lantarki babu dalilinta. Yau ma haka muka kwana babu wutar, saboda haka ban iya samun labaru ta hanyoyin da na saba samu ba. Yanzun haka karfe uku da minti goma sha biyu na dare ba wutar. Wayar tawa ma da nake wannan rubutu da ita tana shirin mutuwa. Ko yaushe talaka zai daina biyan kudin zama a duhu ne oho!
  2. Jiya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan sabon kasafin kudi na shekarar dubu biyu da ashirin da aka yi wa kwaskwarima ya dawo naira tiriliyan 10.8 ya zama doka.
  3. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu, da nada Mohammed Umar da hotonsa ke kasan labarin nan ga wadanda suke iya ganin hoto a labarun nan ke nan, don rike hukumar har a kammala binciken Ibrahim Magu a kuma ga me zai biyo baya.
  4. Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Magu, ya nemi shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu ya ba da belinsa ko don matsayinsa. Ya nemi haka ne ta hannun lauyansa, inda ya ce tun litinin da ya fara hallara gaban kwamitin shugaban kasa da ke bincikarsa yake tsare a hannun ‘yan sanda bai leka gida ba.
  5. ‘Yan Nijeriya su dari biyu da saba’in ne aka kwaso su daga kasar Masar kuma an duba lafiyarsu an ga ba wanda ya harbu ko ya taho da tsarabar kwaronabairos a cikinsu.
  6. Hukumar Imigireshan ta kasa ta hana wasu likitoci ‘yan Nijeriya su hamsin da takwas daga wa zuwa Landan, daga Nijeriya, haka jirgin da suka dauko shatarsa kwasarsu ya juya Landan ba ko dayansu a cikinsa.
  7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata uku ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi, ba amo ba labari.
  8. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari biyar da saba’in da biyar a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 224
Oyo 85
Abuja 60
Ribas 49
Kaduna 39
Edo 31
Inugu 30
Delta 11
Neja 10
Katsina 9
Ebonyi 5
Gwambe 3
Jigawa 3
Filato 2
Nasarawa 2
Barno 2
Kano 1
Abiya 1

  • Toh! Kano daya tal tilo, Kaduna kuma talatin da tara?

Jimilar wadanda suka harbu 31,325
Jimilar wadanda suka warke 12,795
Jimilar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 709
Jimilar wadanda ke jinya 17,819.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Wata ke mun korafin akwai wasu ma’aikatan jihar Kaduna da aka musu ritayar dole a lokacin da wannan gwamnatin ta El-Rufai ta hau, kuma har yau ba a biya su hakkokinsu da fanshonsu ba. Haka nan na ji ‘yan kasuwa da ke da rumfuna a kasuwannin jihar Kaduna da aka rufe saboda tsoron kwaronabairos, na rokon gwamnati ta bude musu kasuwannin.

Za a iya labarun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://www.facebook.com/2356865571252507/posts/2647959155476479/
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply