Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, ashirin da hudu ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabwa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha hudu ga watan Agusta, shekarar dubu biyu da ashirin.

1.Da fatan za a gafarce ni jiya na tintiben alkalami na rubuta watan Oktoba, maimakon Agusta, kodayake wani da ya ga kuskuren ya ja hankalina, na gyara a fesbuk, amma na wasaf ban bi na gyara ba.

  1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani bene mai hawa goma sha bakwai ta intanet, wanda shalkwata ce ta hukumar bunkasa kayayyaki namu na cikin gida a Yeneguwa ta jihar Bayalsa.
  2. Gwamnatin Tarayya ta roki manyan kasashen duniya da su yi watsi da bata sunan da wasu ke yi wa Nijeriya su sayar mata da makamai don yakar ta’adanci da ke damunta.
  3. Karfe biyun daren nan na juma’a na yi, wanda a lokacin ne na fara wannan rubutu suka dauke wutar lantarki, sauro mazansu da matansu suka mun taron dangi. Sai dai gadar minti shida suka yi a kaina, aka dawo da wutar. Sai wani nanataccen sauro ne daya ya ci gaba da mun kuwwa a kunne.
  4. Hukumomin soja sun ce ba sa daukar ankararwar da Amurka ta yi wa Nijeriya cewa ‘yan ISIS da ‘Yan Alka’ida na tuttudowa kasar nan da wasa.
  5. Ministar ayyukan jinkai da jin dadin jama’a Hajiya Sadiya Umar Faruq, ta ce ana nan ana shirin samar da wata cibiya ta kula da bukatun tsofaffi a kasar nan.
  6. Majalisar Koli da Al’amuran Addinin Musulunci ta Kasa reshen jihar Kaduna, ta bai wa musulmi da wanda ba musulmi ba da ke kudancin jihar Kaduna hakurin su zauna lafiya da juna domin babu wani da ya isa ya kori wani daga yankin ya ce shi kadai yake da ‘yanci ko ikon zama.
  7. Sojoji sun ce sun kai dakaru na musamman kudancin jihar Kaduna don tabbatar da zaman lafiya a yankin.
  8. Hukumar gidajen rediyo da talabijin ta kasa NBC ta ci gidan rediyon Nigeria Info 99.3 FM da ke Legas tarar naira miliyan biyar saboda hirar da ya yi da tsohon mataimakin babban gwamnan bankin Nijeriya Obadia Mailafiya, da a hirar ya yi zargin akwai wani gwamna wanda shi ne kwamandan kungiyar Boko Haram.
  9. A shekaranjiya laraba wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum a kalla goma sha biyar a Ukuru karamar hukumar Mariga, wacce rana ce ta cin kasuwar Marigar da ke jihar Neja.
  10. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace, ba shiga ba fita saboda ballewar gadar da sukan samu su haura, da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzu, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi, zai gyara musu, ga wa’adinsa na shirin karewa har yau bai gyara musu ba.
  11. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata biyar ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi har yau shiru. Haka nan wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, ni bin albashin wata daya, wasu wata biyu, wasu wata uku, wasu wata hudu har biyar. Kodayake wasu na cewa gwamnatin ce ta yi BUROK.
  12. Yanzun karfe hudu da minti ashirin na asubah agogon wayata da nake wannan rubutu da ita, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 373 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 69
Oshun 41
Kaduna 40
Oyo 40
Abuja 35
Filato 22
Ribas 19
Kano 17
Ondo 17
Ogun 15
Abiya 14
Gwambe 12
Imo 9
Inugu 7
Kwara 6
Delta 5
Neja 2
Barno 1
Bauci 1
Nasarawa 1

Jimillar da suka harbu 48,116
Jimillar da suka warke 34,309
Jimillar da ke jinya 12,841
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 966

Sai dai kamar yadda na yi bayani rannan su jihar Kogi gwamnansu Yahya Bello ya ‘yanta su daga cutar kwaronabairos. Kasuwanni na bude, makarantu na bude, masallatai da coci na bude, ba takunkumi, ba wanke hannu, ba tazara, ba sabbin harbuwa, ba wadanda suka warke, ba wadanda ke jinya, ba mai mutuwa duk da sunan kwarona. Su biyu ne kadai a duk Nijeriya ba sa sa takunkumi. Shugaban Kasa Buhari, da Gwamna Yahya Bello.

Mu wayi gari lafiya, mu yi juma’a lafiya, kuma Allah Ya raba mu da sharrin mutum, musamman wanda kuke tare ka amince masa Amin.

Af! A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe, don duba shafukana da ke dauke da labarun da na kawo muku daga jumar’ar da ta gabata, zuwa jiya alhamis.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply