Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin ashirin ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hiijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma ga watan Agusta, shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Gwamnan jihar Barno Farfesa Zulum ya taimaka wa hukumomin tsaro na jihar da motoci na sintiri guda dari biyu.
 2. Gwamnan jihar Barno Farfesa Zulum ne ya zama shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa Maso Gabashin kasat nan, tare da alkawari za su bullowa matsalar tsaro ta bayan gida.
 3. Kiristocin jihar Kaduna sun taru a Kaduna don yi wa kudancin jihar Kaduna addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya a yankin.
 4. Kiristoci na jihar Legas sun samu damar zuwa coci jiya lahadi, bayan kusan wata biyar ba zuwa saboda dokar kulle ta kwaronabairos.
 5. Wasu ‘yan Nijeriya na ci gaba da korafin an ki bude musu kasuwanni da barinsu su yi sallolin nan biyar a jam’i, amma gwamnonin da suka hana su, sun yi cincirindo shekaranjiya wajen yakin neman zaben fasto Osagie Ize-Iyamu don zama gwamnan jihar Edo, ba tazara, yawancinsu kuma ba takunkumi. Haka aka taru wajen jana’izar Kashamu ba ruwan manya da kwaronabaros a cakude, sai talaka.
 6. Wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin watansu biyar, wasu wata hudu, wasu uku wasu daya ba albashi babu dalilinsa, kamar yadda ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, ke ci gaba da korafin shekara daya da wata kudsan na biyar ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi, har yau shiru ba amo ba labari.
 7. ‘Yan sanda sun ceto wasu shanu talatin daga hannun ‘yan bindiga a jihar Katsina.
 8. Kungiyar ECOWAS ta raya tattalin arzikin yammacin Afirka, da wasu kungiyoyin sun ceto wasu magidanta hamsin masu bukatar agaji, ta hanyar ba su dabbobi a jihar Kabbi.
 9. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da kasancewa a killace ba shiga ba fita daga kauyen saboda ballewar gadar da sukan samu su haura, da shugaban karamar hukumar, Jaja, ya musu alkawarin idan sun zabe shi, zai gyara musu gadar, ga wa’adinsa na shirin karewa ya kasa gyara musu.
 10. Gwamna Orton na jihar Binuwai ya ki wani tayi da aka masa na ya koma jam’iyyar APC.
 11. A Berut an kashe wani dan sanda a ci gaba da zanga-zangar da jama’a ke yi sakamakon fashewar wani abu a Labanan da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da dari da hamsin.
 12. Wasu rahotanni na nuna wadanda suka harbu da kwarona a Amurka sun kai mutum miliyan biyar.
 13. Yanzun karfe hudu da minti biyar agogon Kinkinau a Kaduna Nijeriya, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 437 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 107
Abuja 91
Filato 81
Kaduna 32
Ogun 30
Kwara 24
Ebonyi 19
Ekiti 17
Oyo 8
Barno 6
Edo 6
Kano 4
Nasarawa 3
Oshun 3
Taraba 3
Gwambe 2
Bauci 1

Jimillar da suka harbu 46,577
Jimillar da suka warke 33,186
Jimillar da ke jinya 12,446
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 945

 1. Bankuna da dama da ke misali a nan jihar Kaduna na ci gaba da rufe rassansu, a wani abu mai kama da durkushewarsu saboda matsalar kwaronabairos, ga kasuwanni a kulle babu hada-hadar kudi sosai duk sai tarin bashi.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Daya daga cikin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta kasa wato NUJ, ya mun korafin idan na tashi jero gidajen talabijin da rediyo da na horas musu da ma’aikatansu, nakan manta da kungiyar ta NUJ da ta taba gayyata na horas da ‘ya’yan kungiyar. To a yi hakuri na tuba kuma yau ga kungiyar a sama a jerin wadanda na horas musu da ma’aikata, har na ba su takardar shaida, da wasunsu ke amfani da ita wajen neman karin girma, da kuma samun aiki a wasu gidajen rediyo ko talabijin a ciki da wajen Nijeriya. Ga su:

i. N.U.J.
ii. F.R.C.N.
iii. N.T.A.
iv. KSMC RADIO
v. DITV/ALHERI RADIO
vi.NewAge Network
vii. LIBERTY RADIO
viii. KASU F.M. RADIO
ix. FREEDOM RADIO
x. NAGARTA RADIO
xi. KADUNA MEDIA ACADEMY
xii Mass Communication Students,
Kaduna Polytechnic.

Wannan dama ce ga duk gidan rediyo ko talabijin ko jarida da sauran kafofi na watsa ko yada labaru da ke bukatar in horas musu da nasu ma’aikatan, su tintibe ni. Babu tsada.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply