Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, goma sha tara ga wata Zulhijja shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da tara ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Hihihi. Hahaha. Huhuhuhu. Hohoho. Hehehehe. Siyasa muguwar wasa. Yanzun kallo ya koma jihar Edo. Da farko dai Amurka ta nuna damuwarta da irin wainar da ake toyawa a siyasar jihar Edo, da za a yi zaben gwamnanta a watan gobe. Na biyu jagoran APC Ahmed Tinubu ya ce gwamnan jihar Edo Obaseki ya aikata laifin da ya cancanci tsigewa daga kan kujerarsa. PDP ta mayarsa masa da martanin cewa tuni ta gano Tinubu ne ke kulla tibbun rigima a jihar ta Edo. Na uku ministan shari’a Malami, ya umarci shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya bai wa ‘yan majalisar dokoki na jihar Edo su goma sha bakwai da suka sauya mazaunin majalisar zuwa wani gida har suka tsige shugaban majalisar. Sai dai PDP ta jihar ta ce babu wata shedara ta kundin tsarin mulkin kasar nan da ta ba Malami ikon umartar shugaban ‘yan sanda ya kare irin wadannan mutane da tuni suka rasa kujerarsu ta majalisa saboda sun kai wasu kwanaki ba sa zuwa zaman majalisar. Sannan a ta daya bangaren mataimakin gwamnan jihar Edo ya ce wasu sun shirya tsaf don kashe wasu daidaikun jama’a a jihar ta Edo. Kuma da ma hukumar zabe ta kasa ta ce ba za ta yi wata-wata ba wajen dage zaben gwamna na jihar idan ta ga zai zama rigima. To wai me ya sa zaben jihar Edo ya fi daukar dimi ne haka?
  2. Wasu matasan kudancin jihar Kaduna sun yi zanga-zangar korafi a kan matsalar tsaro a kudancin jihar Kaduna.
  3. Gwamnatin jihar Kano ta yi feshi a makarantu dari biyar da ashirin da takwas a shirye-siryenta na bude makarantun boko.
  4. An kwaso karin ‘yan Nijeriya dari uku da ashirin da biyar daga Amurka, da wasu daga Sudan da Ingila.
  5. Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce ya fi goyon bayan a ci gaba da tsarin karba-karba na mulkin kasar nan, wato a bar wa kudu mulkin kasar a zaben shekarar 2023.
  6. Wadanda suka harbu da kwaronabairos a Afirka sun haura miliyan daya.
  7. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata hudu ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi har yau shiru. Sannan wasu malaman jami’a watansu biyar ke nan babu albashi, wasu kuma wata biyu wasu wata daya.
  8. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da zama a killace saboda karyewar gadar da suka saba haurawa su shiga ko su fita, wacce a lokacin yakin neman zabe, shugaban karamar hukumar ta Kudan, Jaja, ya musu alkawarin idan suka zabe shi zai gyara musu. Ga wa’adinsa na shirin karewa ya kasa gyara musu.
  9. Yanzun karfe hudu da minti goma ga wani zakara can da ya tsallake rijiya da baya a sallar nan da ta wuce bai sha wuka ba na cara, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 453 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Abuja 75
Legas 71
Binuwai 53
Delta 39
Barno 30
Inugu 25
Filato 24
Oshun 20
Abiya 19
Oyo 17
Kaduna 16
Kano 13
Ebonyi 13
Ogun 9
Kwara 7
Ondo 6
Gwambe 3
Akwa Ibom 1
Ribas 1

Jimillar da suka harbu 46,140
Jimillar da suka warke 33,044
Jimillar da ke jinya 12,153
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 943

Mu wayi gari lafiya.

Af! Wuraren karfe uku saura minti biyar na daren nan ina kan rubuta wadannan labaru, a daidai lokacin nake kwafo alkaluman wadanda suka harbu da kwaronabairos daga dandalin cibiyar dakile yaduwar kwaronabairos ta kasa da ke fesbuk, na gama da jihar Kwara zan shiga jihar Ogun sai biron da nake aiki da shi ya kare. Wato ruwan ko in ce tawadar tasa ta kare. Da yake sai na kwafe a takardar kafin in Hausantar da alkaluman a rubutun nawa. Duk na gama laluben kusuwar da nake tunanin zan samu ko da fensir ne babu. Na fita cikin daren na nufi dakin samari, ina taba kyaurensu suka ce wane ne? Na ce ni ne biro nake nema, suka ce wani makwabcinmu ya zo ya ara da rana bai dawo da shi ba. Nan ita ma Madam ta bazama neman fensir a cikin gida, aka yi sa’a aka samu, sai dai matsalar fensirin ba a feke yake ba. Aka lalubi jakar yara ba shafina na feke fensir. Aka bazama neman reza, da kyar aka samu wata sai dai ba ta da kaifi. Haka na zauna ina feke fensirin da jiibin goshi. Da yake fensirin irin na zamani ne mai amaja, ina fekewa tsinin rubutun yana karyewa. Haka na lallaba na feke shi. Na soma rubutu amma dishi-dishi yake yi, in na danna da karfi ya kuma karyewa. Haka na ci gaba da lallabawa na iya rubuta jihar Ondo, da Gwambe, da Akwa Ibom, da Ribas, da sauran Jimillar wadanda suka harbu da wadanda suka warke da sauransu.
Na kawo wannan misali ne don a san daya daga cikin kalubalen da nakan fuskanta cikin dare zuwa asuba a kullum.
Sauran sun hada da karewar data bayan na kammala rubutu, ko rashin wuta, ko gyangyadi, ko tutsun waya, ko tutsun soshiyal midiya, ko sauro, ko zafi, ko jiran tabbaci ko sahihancin labari, da dai sauransu. Wani lokaci sai na saki rubutun da asubah, sai ka ga wani ya soma cin gyarata ko a labarin ko a rubutun bayan na gama cin kwakwa wajen hana idona bacci don hada labarun.

Yanzun karfe hudu da rabi da minti daya na asubah, na kammala na kuma saki rubutun na yau. Ga dirin motar masu ruwan fiyawata can na ji ta wuce.

Za a iya leka rubutun labarun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2671432666462461&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply