Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, goma sha takwas ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa, kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da takwas ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Bayan an kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari dan takaran gwamnan jihar Edo karkashin inuwar jam’iyyar APC Fasto Osagie Ize, shugaban kasa ya sa masa albarka da kiran a zabi Osagie gwamna jihar Edo.
- Dan takaran gwamnan na jihar Edo karkashin APC Fasto Osagie, ya ce ba a gidansa ‘yan majalisar dokoki ta jihar Edo suka gudanar da taron tsige shugaban majalisar ba. Ana nan dai ana ci gaba da takaddama tsakanin APC da PDP a kan zaben gwamna na jihar Edo, da rikicin majalisar dokoki ta jihar.
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan sabuwar dokar shekarar nan da ta yi gyara ga kamfanoni da batutuwan da suka shafe su, bayan kusan shekara talatin ba a yi wa dokar kwaskwarima ba, sai yanzun.
- An kwaso ‘yan Nijeriya su dari uku da talatin da daya daga Daular Larabawa zuwa gida Abuja.
- An bude masallatan juma’a jiya, musulmi suka yi Sallar Juma’a bayan kusan wata biyar ba a yi Sallar ba a jihar Legas.
- Mamallakin fesbuk Zuckerberg ya zama na uku a kudi a duniya.
- A makon gobe gwamnatin tarayya za ta soma biyan ma’aikatan lafiya wani alawus da suke ta korafi a kai wato ‘Hazard Allowance’
- Mahukunta jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsenma a jihar Katsina, sun bukaci ma’aikatan jami’ar su daina zuwa aiki harabar jami’ar saboda matsalar tsaro ta ‘yan bindiga da ta ki ci ta ki cinyewa a al’umomin da ke makwabtaka da jami’ar.
- Wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya, watan su na biyar ke nan ba a biya su albashi ba, ga ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i, shekararsu daya da wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi ba amo ba labari.
- Mutanen kauyen Guibi da ke karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can a killace ba shiga ba fita, sakamakon ballewar gadar da sukan samu su haura, da shugaban karamar hukumar, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi wa’adinsa na shirin karewa har yau ya kasa gyara musu.
- Wata kotu a Abuja ta ci Naira Marley tarar naira dubu dari biyu saboda saba wa dokar kulle, da ta sa takunkumi, da ta bai wa juna tazara da cincirindo.
- Ingila ta gargadi jama’arta da ke kasar nan su kiyayi wasu jihohi ashirin da daya na kasar nan saboda matsalar tsaro a jihohin da suka hada da kidinafin da sauransu.
- Yanzun karfe hudu da rabi na asubah da nake wannan rubutu akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 443 a jihohi da alkalumma kamar haka:
Filato 103
Legas 70
Abuja 60
Ondo 35
Edo 27
Ribas 27
Kaduna 20
Oshun 19
Barno 18
Oyo 18
Kwara 11
Adamawa 9
Nasarawa 7
Gwambe 6
Bayelsa 4
Imo 4
Bauci 2
Ogun 2
Kano 1
Jimillar da suka harbu 45,687
Jimillar da suka warke 32,637
Jimillar da ke jinya 12,114
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 936
Mu wayi gari lafiya.
Af! Allah Ka raba mu da sharrin mutum Amin.
Za a iya leka rubutun labarun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.