Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, goma sha biyar ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikimakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyar ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da goma sha biyar.

 1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake nuna damuwarsa da matsalar tsaro da ke ci gaba da addabar kasar nan, tare da ba da umarnin a yi wa tsarin na yanzun garambawul. Sai dai jama’a na ta kokarin gano wane ne shugaban kasa a matsayinsa na babban kwamandan askarawan kasar nan yake ba wannan umarmi. Kansa yake ba, ko Osinbanjo ko Ahmed Lawan ko Gbajabiamila ko Boss Mustapha, ko Mongunu ko manyan shugabannin bangarorin tsaron da ake ta matsa masa ya fatattake su?
 2. Yau katafanin gwamnonin Nijeriya za su gudanar da wani taro, cikin abubuwan da za su tattauna har da tabarbarewar tsaro da batun bude makarantu.
 3. Gwamnatin Tarayya ta kara yawan kudin tarar da za a yi wa wanda ya yi kalaman kiyayya daga naira dubu dari biyar wato rabin miliyan, zuwa naira miliyan biyar.
 4. Gwamnatin jihar Gwambe ta ba hukumomin sojan sama gudunmawar fili kadada dari biyu da talatin domin yin sansanin sojan sama a wajen, don agawa tsaro a Arewa Maso Gabashin Kasar nan
 5. Gwamna Badaru na jihar Jigawa ya umarci dukkan ma’aikatan jihar kowa ya koma bakin aiki yau, saboda wajen kwana goma sha daya ke nan ba a ji duriyar sabon harbuwa da kwarona a jihar ba.
 6. Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce babu mamaki ya sake sanya dokar kulle gabadaya a jihar Kaduna saboda jama’ar jihar na yawo da takunkuminsu a aljihu maimakon a fuska. Kuma da ya bude kasuwa ‘yan kasuwa su mutu, gara ya ci gaba da kullewa su ci gaba da barar da aka ce sun koma suna yi a yanzun haka.
 7. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Hukumar Raya Yankin Neja Delta ta biya dalibai kudinsu na tallafin karatu wato sikolashif.
 8. Mataimakin gwamnan jihar Kwara da matarsa sun harbu da kwarona.
 9. A bana kasar Saudiya ta yi asarar dala biliyan goma sha biyu saboda rage yawan masu zuwa sauke farali saboda kwarona.
 10. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojij ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi, ba amo ba labari.
 11. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna sun kasance cikin kullen dole saboda ba sa iya fita daga kauyen ko shigarsa, saboda lalacewar gadar tsallakawa kauyen, da shugaban karamar hukumar ta Kudan ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa ba amo ba labari.
 12. Yanzun karfe hudu na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwarona 304 a jihohi da alkalumma kamar haka:

Abuja 90
Legas 59
Ondo 39
Taraba 18
Ribas 17
Barno 15
Adamawa 12
Oyo 11
Delta 9
Edo 6
Bauci 4
Kwara 4
Ogun 4
Oshun 4
Bayelsa 3
Filato 3
Neja 3
Nasarawa 2
Kano 1

Kaduna ????
Kogi ????

Jimillar da suka harbu 44,433
Jimillar da suka warke 31,851
Jimillar da ke jinya 11,672
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 910

Mu wayi gari lafiya.

Af a jerin wadanda suka yi tsokaci a rubutuna na jiya tsokacin Usman Aburajab ne ya fi daukar hankalina kamar haka:

‘ALLAH yakara hazaka . Mallam Yan fensho na kana hukumomi jihar Kaduna tare da malaman kanaan asibitoci da kuma malaman makarantùn firamerai . Dukkan su basuyi sallah da kudin alawansu da albashi ba’

Sai bidiyo da ke biye ga wadada ke iya ganin bidiyo a rubutuna, hira ce da tashar KSMC Kaduna State Media Corporation wato Hukumar Watsa Labaru ta jihar Kaduna ta yi da ni kai tsaye ta talabijin da rediyo shekaranjiya da daddare, a kan yadda kwarona ta shafi bikin sallar bana.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskaf Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2668122203460174&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya

Labarai Makamanta

Leave a Reply