Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, goma sha takwas ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Kwamitin shugaban kasa da ke yi wa Ibrahim Magu mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC tambayoyi a kan zargi daban-daban da ake masa, ya bai wa daraktoci da shugabanni sassa na hukumar, mako daya su tarkato masa fayil-fayil na bayanan kudade da kaddarori da hukumar ta karbe, daga shekarar dubu biyu da goma sha biyar zuwa yanzun. Bayanai na nuna ‘yan sanda na ci gaba da tsare Magun.
  2. Mataimakin shugaban kasa Osinbanjo ya ce sharri aka yi masa aka ce ya karbi wasu kudade daga hannun Ibrahim Magu, da bayanin cewa zai dauki mataki a kan wanda ya kago wannan kage da aka masa.
  3. A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanya hannu a kan sabon kasafin kudi na shekarar nan ta dubu biyu da ashirin da aka yi wa kwaskwarima ya koma naira tiriliyan goma sha daya ba wasu mutsamutsai (tiriliyan10.8), ya zama doka.
  4. Babban lauyan gwamnatin jihar Nasarawa ya harbu da kwaronabairos.
  5. Nijeriya ta kera tata na’urar gwajin gano masu kwaronabairos da ta fi ta turawa sauri da inganci ga rahusa da saukin samu.
  6. Majalisar wakilai na ci gaba da korafi a kan walawalar bangaren wutar lantarki, mu ma dai wutar ba ma ganinta sai cikin dare. Haka muke yini babu ita babu dalilinta.
  7. Kwamitin majalisar dattawa na nan yana bin diddigin wasu makudan kudi da ake zargin wasu sun wawure su a hukumar NDDC ta kula da raya yankin Neja Delta.
  8. Hukumomin sojan Nijeriya sun ce a ‘yan kwanakin nan sun kashe mahara saba’in da biyar a yankin Arewa Maso Gabashin kasar nan, da hamsin da takwas a Arewa Maso Yammacin Kasar nan.
  9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata uku suna dakon ariyas na sabon albashi, har yanzun shiru. Sai dai na ji wasu sun ce sun ga jadawalin yawan kudaden ariyas din, duk an zabge musu kudaden da sunan wasu kudade na haraji tsugugu da na tanadin gida na tilas, da sauransu da aka cire musu da karfi da yaji, abin da ya yi saura da za a ba su bai taka kara ya karya ba.
  10. Jiya da daddare kafin in kwanta bacci, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari hudu da casa’in da tara a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 157
Edo 59
Ondo 56
Oyo 31
Akwa Ibom 22
Barno 21
Filato 19
Kaduna 18
Katsina 18
Bayelsa 17
Abuja 17
Delta 14
Kano 11
Ribas 10
Inugu 8
Ogun 6
Kwara 4
Imo 3
Nasarawa 2
Oshun 2
Abiya 1
Ekiti 1
Neja 1
Yobe 1

Jimilar wadanda suka harbu 30,768
Jimilar wadanda suka warke 12,546
Jimilar wadanda suka riga mu gidan gaskiya 689
Jimilar wadanda ke jinya 17,513

Kada a manta yau juma’a a nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito da safiyar nan da shafukan da ke dauke da labarun da na rubuta, daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Njjeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply