Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, goma sha hudu ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da hudu ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Jiya da safe wuraren karfe bakwai sai ga rahoto ya ishe ni cewa ma’aikatan kwalejojin foliteknik sun soma jin dilin-dilin da ke nuna lissafin watansu na albashi ya daidaita yau hudu ga watan Agusta. Sai dai watan ariyas da suke bi shekara daya da wata hudu ne bai daidaita ba har yau.
  2. Yau makarantu na sakandare da dama ke budewa don komawar dalibai da ke ajin karshe, don shirye-shiryen rubuta jarabawar fita ta WAEC.
  3. Kamfanin jiragen sama na AIR PEACE ya sallami direbobinsa na jiragen sama su sittin da tara daga aiki saboda kwaronabairos.
  4. Kiristoci na kudancin jihar Kaduna, sun yi kira ga kiristocin su gudanar da addu’a da azumi na wata daya, domin rokon Allah Ya kawo karshen kashe-kashen da ake yi kudancin jihar Kaduna.
  5. Gwamnoni na jihohin Nijeriya sun nuna suna tare da gwamnan jihar Barno Babagana Zulum sakamakon harin da aka kai masa, da shi Zulum ke zargin sojoji ne suka kai masa hari ba ‘yan kungiyar Boko Haram ba.
  6. A jihohin kasar nan, a jihar Taraba ne kadai babu wani rahoto da ke nuna wani ya riga mu gidan gaskiya samakon kwarona.
  7. EFCC ta kara yawan tuhume-tuhumen da take yi wa Mohammed Adoke.
  8. Yanzun karfe hudu da minti biyu na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 288 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 88
Kwara 33
Oshun 27
Abuja 25
Inugu 25
Abiya 20
Kaduna 17
Filato 13
Ribas 13
Delta 10
Gwambe 8
Ogun 4
Oyo 3
Katsina 1
Bauci 1

Jimillar harbuwa 44,129
Jimillar da suka warke 20,663
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 896
Jimillar da ke jinya 22,570

Mu wayi gari lafiya.

Af! A yanzun dai ta tabbata babu hanyar shiga ko fita kauyenmu Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan saboda dan gefen gadar da mukan dan samu mu raba don wucewa ya rifta. Gada ce da na dade ina korafi akanta. Kuma an ce tana daga cikin alkawuran da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun ya daukar wa mutanen Guibi cewa idan sun zabe shi zai gyara. Har yau shiru ya kasa gyara mana gadar.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2667315400207521&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply