Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, goma sha uku ga wata Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da uku ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. Sai dai su ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, har yau ba su shiga watan Agusta ba, suna nan a watan Yuli talatin da hudu da shi. Saboda ba su ga albashin ko dilin-dilin na watan Yuli ba, haka aka yi Sallah, aka yi layya duk suna kallo, kuma da ma shekara daya da wata hudu suna jiran ariyas.
  Har na ji wani yana cewa da Jonathan ne shugaban kasa aka ce an yi Sallah haka babu albashi wai! Hmm ! bakina da goro.
 2. Yau ma’aikata ke komawa bakin aiki bayan hutun Sallah da gwamnatin tarayya ta bayar, alhamis da juma’a. Har na ji wani yana cewa a yau da kowa ke komawa bakin aiki, ‘yan kasuwa da aka kulle musu kasuwanninsu a jihar Kaduna, su zaman gidan bai kare ba tukuna. Wai! Hmm! Bakina da goro.
 3. An tura karin sojoji da ‘yan sanda hanyar Kaduna zuwa Abuja don maganin kidinafas, inda ‘yan sanda suka ce babu gaskiya a labarin da ake yadawa cewa kidinafas sun dawo hanyar har sun soma kidinafin.
 4. Kungiyar kare hakkin bil’Adama ta SERAP a takaice, ta bukaci gwamnatin tarayya ta wallafa bayanin basussukan da ta ciyo/ciwo daga shekarar dubu biyu da goma sha biyar zuwa yau.
 5. An kwaso ‘yan Nijeriya dari da goma sha bakwai daga Yuganda, da Ruwanda da Tanzaniya.
 6. Ganduje na jihar Kano ya yi wa wasu fursunoni 43 afuwa da sallar nan.
 7. Gwamna Zulum na jihar Barno ya ce wasu ke yin zagon kasa ga kokarin kawo karshen masu kai hare-hare a Arewa Maso Gabashin kasar nan da sai shugaban kasa Buhari ya yi da gaske bangaren tsaro.
 8. Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta NHRC ta ce akwai take hakkin dan Adam gudu 321 kuma kashi casa’in cikin dari na adadin ‘yan sanda ne suka aikata.
 9. ‘Yan sanda na bincike a kan mutuwar wasu mata bakwai a wani wajen gyaran gashi da ke jihar Neja.
 10. Fitaccen afton nan na fina-finan Indiya Amitabh Bachchan ya warke daga kwaronabairos.
 11. Yanzun karfe hudu da minti tara na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwarona mutum 304 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 81
Abuja 39
Abiya 31
Kaduna 24
Ribas 23
Filato 16
Kuros Ribas 13
Ebonyi 12
Ondo 12
Ekiti 11
Edo 11
Binuwai 10
Nasarawa 10
Ogun 6
Gwambe 5

Jimillar da suka harbu 43,841
Jimillar da suka warke 20,308
Jimillar da ke jinya 22,645
Jimillar gidan gaskiya 888

Mu wayi gari lafiya.

Af! A rana mai kamar ta yau 3/8/2015 shekara biyar daidai na yi wannan rubutu da ke biye a dandalina na fesbuk kamar haka:

‘Ni ma dai wannan rakiya ko rufa wa matar shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki baya da wasu ‘Yan Majalisar ta Dattawa da ta Wakilai ciki har da Dino Melaye suka mata zuwa Hukumar EFCC da ke tuhumarta da laifin wawurar kudin kasa abin kunya ne da zubar da girman ‘Majalisun biyu.Wannan ya nuna karara cewa ‘Yan Majalisun biyu suna daure gindin matan manyansu su saci dukiyar kasa ba abin da zai faru. Aikin da aka zabi ‘Yan Majalisa su yi ke nan gadin matan shugabanninsu zuwa amsa tuhuma? A she dama haka Dino Melaye yake? Lallai kam kowanne gauta ja ne sai fa in bai sha rana ba’

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi fa ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply