Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, goma sha biyu ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyu ga watan Agusta na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Sai dai su ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, su suna cikin watan YULI 33 da shi ba su shiga watan AGUSTA ba tukuna, saboda har yau babu albashin watan YULI. Haka suka yi Sallah, aka yi layya suna kallo. Da ma shekararsu daya da wata hudu suna dakon ariyas na sabon albashi har yau shiru kamar an shuka dusa.
  2. Wasu musamman masu kare hakkin mata, na ta cewa ba su ji dadin yadda kotu ta yi watsi da karar sanata Abbo da ‘yan sanda suka kai suna tuhumarsa da cin zarafin wata mata a wajen sayayya ba. Kotun ta ce ta yi watsi da karar ce saboda ‘yan sanda sun kasa gabatar da kwararan shaidu a kan zargin da suke masa. Kotu ta ce ko hakurin da aka ga sanata Abbo ya ba matar ta gidajen talabijin, ba yana nufin ya aikata laifin ba ne.
  3. ‘Yan Nijeriya su dari uku aka kuma kwasowa daga Amurka, da ke nuna an kwaso ‘yan Nijeriya su dubu daya, da dari hudu da talatin ke nan daga Amurka.
  4. Wasu mata daga Labanan da aka nuna a talabijin na rokon a kwasosu zuwa gida Nijeriya, an kwashe su ne aka kai su can yin bauta.
  5. A jihar Nasarawa an yi kidinafin wani basarake aka kashe shi.
  6. Zuwa yanzun an yi wa ‘yan Nijeriya su dubu dari uku gwajin kwaronabairos.
  7. Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya warke daga kwarona bayan jinyar kwana goma sha daya.
  8. Gwamnatin jihar Legas za ta bude duk wuraren ibada daga ranar bakwai ga watan nan, da sassauci ga gidajen cin abinci, da kara yawan jama’a da ke iya taruwa wuri guda daga 20 zuwa 50.
  9. Yanzun karfe uku na dare, akwai sabbin harbuwa da kwarona 386 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Abuja 130
Legas 65
Ondo 37
Osun 29
Filato 23
Ribas 15
Inugu 14
Nasarawa 12
Bayelsa 11
Ebonyi 11
Ekiti 9
Oyo 8
Edo 8
Abiya 6
Ogun 3
Katsina 3
Imo 1
Adamawa 1

Kaduna ???

Jimillar da suka harbu 43,537
Jimillar da suka warke 20,087
Da suka riga mu gidan gaskiya 883
Da ke jinya 22,567

Mu wayi gari lafiya.

Af! A rana mai kamar ta yau wayo 2/8/2016 shekara hudu daidai na yi wannan rubutu da ke biye a dandalina na fesbuk:

‘Yau so nake in tabo fassarar kalmar ‘PADDING da ‘yan majalisar wakilai suka yi wa kasafin kudin shekarar nan bayan Baba Buhari ya kai musu don neman amincewarsu. Dan majalisa Jibrin yake ta tonon silili bayan shugaban majalisar Dogara ya tsige shi daga kan shugabancin kwamitin kasafi na majalisar. Ina ganin da Bukola zai yi kuskuren tsige nasu shugaban kwamitin kasafin da shi ma an soma masa fallasar PADDING din da suka aikata. Wai ma ina fassarar PADDING da Hausa? Gidajen rediyo da talabijin da intanet da jaridu kowa yana ta yin tasa fassarar dai-dai fahimtarsa. Wasu su ce Maho, wasu badakala, wasu kumbiya-kumbiya, wasu aringizo wasu hadama, wasu sakalewa, wasu coge, wasu dunzugu, wasu ciko, wasu face-face, wasu toliya, wasu sagale, wasu goyo, wasu lankaye, wasu kulumbutu, wasu angizo, wasu cushe, wasu zurmugudu, wasu fasakwauri, wasu cushe-cushe, wasu ciko, wasu waskiya da dai sauransu. Wannan ke nuna cewa Hausa na kara bunkasa fiye da yadda ake zatto tunda tana da zakakurai kuma fasihai da a kullum suke kokarin kararta da kalmomi sababbi. Kuma muhawara ita ce ilmi kuma karuwa ga harshe. Kowanne da ya kawo tasa fassarar ya ba da dalilansa. Misali jiya da safe na ji Abubakar Jidda Usman a shirinsa na hantsi na rediyon Firidom da ke nan Kaduna, ya fassara kalmar da GOYO.Ya ce kamar alhazai ne da ake kayyade musu kayan da za su dauko. Sai su kara da goyo, ka ga hukumomi na ta kwacen goyon saboda an hana amma ga dai Alhaji ya yi. Duk fassarar da kowa ya kawo na yarda da ita amma na fi yarda da goyo zuwa yanzun ban dai san nan gaba ba kuma ra’ayina ne don ni dalibi ne na harshe ba malami ba. Na gode yayana Ladan Waziri’

Sannan a shawagin da na yi jiya a fesbuk, babu hoton da ya fi daukar hankalina da burge ni kamar wanda na sa a kasan rubutuna na yau ga wadanda ke iya ganin hoto a rubutuna, wato hoton tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida da iyalansa.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply