Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, goma sha daya ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da daya ga watan Agusta, shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. A jiya musulman duniya suka hau Idin babbar Sallah tare da yin layya. A nan gida Nijeriya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da sallarsa ta Idi a fadar shugaban kasa da ke Abuja, tare da uwargidarsa Aisha, da diyansu da wasu mukarraban gwamnati, ta kiyayewa da baiwa juna tazara, da sanya takunkumi kamar yadda aka tsara shimfidun sallar don hana harbuwa da cutar kwaronabairos.
 2. An gudanar da sallar idi a filayen idi daban-daban da ke kasar nan har da jihar Kaduna, inda malaman da suka limanci sallolin suka mayar da hankali ga yin kira ga al’umar musulmi a dage da addu’a a kan kwaronabairos, da matsalar tsaro da yin kira ga gwamnatin jihar Kaduna ta tausaya wa ‘yan kasuwa ta bude musu kasuwanninsu.
 3. Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya nuna takaicinsa a game da yadda wadanda ake ba mukaman siyasa ke cin amana. Karon farko yana tsokaci a kan binciken da ake yi a kan Magu da kuma shugabanin rikon kwarya na hukumar raya yankin Neja.
 4. Jiga-jigan majalisar wakilai sun bukaci shugaban kasa ya kori manyan hafsoshin tsaron kasar nan saboda harin da aka kai wa gwamnan jihar Barno Zulum.
 5. Gwamnonin jihohin Arewa sun yi tir da harin da aka kai wa ayarin gwamnan jihar Barno Zulum.
 6. Duk da harin da aka kai wa Zulum, sai da ya iyar da nufinsa na kai wa ‘yan gudun hijira su dubu tamanin kayan abinci a Mongunu don su ji dadin gudanar da shagulgulan Sallah.
 7. An kwaso ‘yan Nijeriya su dari biyu da goma sha biyu daga kasar Masar.
 8. Kungiyar lauyoyi ta kasa ta zabi shugabanta na talatin Olumide.
 9. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna Umar Muri ya tura karin ‘yan sanda kananan hukumomi biyar, Kaura, da Kauru, da Zangon Kataf, da Jama’a da Kajuru don tabbatar da an zauna lafiya da dakatar da kashe-kashe.
 10. Yau daya ga watan Agusta, ga ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, yau watansu na Yuli talatin da biyu, watan bai mutu ba tukuna saboda ba su ji dilin-dilin ba, ariyas ma shekara daya da wata hudu ke nan na sabon albashi har yau babu labari.
 11. Yanzun karfe hudu da minti goma na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 462 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Abuja 93
Filato 64
Kaduna 54
Oyo 47
Ondo 32
Adamawa 23
Bauci 19
Ribas 9
Ogun 9
Delta 9
Edo 7
Kano 6
Inugu 6
Nasarawa 5
Oshun 1

Jimillar da suka harbu 43,151
Jimillar da suka warke 19,568
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 879
Jimillar da ke jinya 22,707

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina kuwa son lekawa kauyenmu Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sai dai an ba ni bayanin cewa babu hanyar shiga saboda gadar nan da nake ta korafi a kanta, ta gagari shugaban karamar hukumar Kudan gyarawa. An ce a lokacin yakin neman zabe, ya yi wa mutanen kauyenmu alkawarin idan an zabe shi zai gyara, ga wa’adinsa na shirin karewa ya kasa gyara gadar.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2664837007122027&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply