Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, jajibarin babbar sallah, tara ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin anabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin ga watan Yuli, shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Gobe take babbar Sallah kuma tuni gwamnatin tarayya ta sanar da ta ba da hutu yau da gobe domin samun damar gudanar da Sallar, har shugaban kasa Muhammadu Buhari ma ya sanar da zai je Daura tare da iyalinsa don yin Sallah a can, da batun ba ya bukatar zuwa masa yawon Sallah ko gaisuwar Sallah saboda hana yada cutar kwaronabairos.
  2. Gobe take Sallah ta layya, da ake sa ran musulmi su sayi raguna da sauran dabbobi da aka amince don yin layya da su, sai dai kash! Da kamar wuya ga wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya irin na kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i domin kuwa har zuwa cikin daren nan da nake wannan rubutu ba su ga dilin-dilin wato albashi ba, ga kuma shekararsu daya da kusan wata hudu ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi.
  3. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartaswa ta kasa da aka saba yi duk laraba, har aka yi tsit na minti guda don juyayin rasuwar mahaifin gwamnan jihar Kwara, da kuma batu a kan wutar lantarki.
  4. Jiya jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja, da Abuja zuwa Kaduna ya dawo da zirga-zirga bayan wata hudu bai motsa ba, saboda kwaronabairos.
  5. Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da al’amuran sojoji Sanata Ndume, ya ce sai sai yana ganin bai dace a wannan lokaci, a ce ana karbar ‘yan kungiyar Boko Haram da suka ce sun tuba, har ana musu gata, da goma sha tara ta arziki, alhali ga ‘yan gudun hijira da ‘yan kungiyar suka kashe musu iyaye, ko maza, ko mata. Ko yara, ko suka kashe sojoji da sauransu na cikin mawuyacin hali da jimami ba.
  6. Wasu ‘yan bindiga sun kai wa ayarin gwamman jihar Barno farmaki a garin Baga, sai dai gwamna Babagana Zulum ya isa Mongunu lafiya lau ba tare da ya ji ko kwarzane ba.
  7. Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta fitar da sabon jadawalin ranakun jarabawa, in da masu rubuta jarabawar NECO za su fara a ranar biyar ga watan Oktoba su gama sha takwas ga watan Nuwamba.
  8. An kwaso ‘yan Nijeriya su 289 daga Amurka zuwa Abuja.
  9. ‘Yan Majalisar Wakilai daga jihar Kaduna sun bayyana cewa sun ji labarin bayan Sallah za a ci gaba da kai wa al’umomin kudancin jihar Kaduna zafafan hare-hare na kare dangi.
  10. Wasu ‘yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Kwaton Karfe da ke jihar Kogi, suka kashe mutum a kalla goma sha hudu.
  11. Zuwa karfe wajen hudu na asubah da nake wannan rubutu, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 404 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 106
Abuja 54
Ribas 48
Filato 40
Edo 29
Inugu 21
Oyo 20
Kano 18
Ondo 15
Ogun 10
Ebonyi 9
Ekiti 8
Kaduna 6
Kuros Ribas 5
Kwara 4
Anambara 3
Delta 3
Imo 2
Nasarawa 2
Barno 1

Jimillar da suka harbu 42,208
Jimillar da suka warke 19,004
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 873
Jimillar da ke jinya 22,331

  1. Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na uku ya hori al’umar musulmi a yi sallar idi a masallatan juma’a don dakile yaduwar kwaronabairos.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Na lura idan yamma ta yi zuwa dare za ka ga manyan motoci na ta gittawa ta baifas sun fito daga hanyar Abuja suna nufa Kawo, ko sun fito daga Kawo suna nufa hanyar Abuja. To jiya a shirin Gari Ya Waye na Rediyo da Talabijin na DITV da Alheri Rediyo da ke Kaduna, na ji direbobin na cewa sukan wuto ne da yamma idan sun daidaici ‘yan kasteliya sun tashi a hanyar. Suka ce ko’ina suna shiga na lungunan kasar nan hankalinsu kwance, amma ban da baifas ta Kaduna saboda kasteliya na matsa musu da tara ta fitar hankali.

Za a iya leka rubutun labarun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply