Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, takwas ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da tara ga watan Yuli na shekarat dubu biyu da ashirin.
- Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun gobe alhamis da jibi juma’a don gudanar da shagulgulan Sallah.
- Yau ashirin da tara ga wata, ma’aikatan kwalejojin foiteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, sun soma cire ran samun dilin-dilin kafin Sallah, kuma da ma ga shi shekara daya da kusan wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban bankin raya Afirka Akinwumi Adesina murnar wanke shi da wani kwamiti mai zaman kansa ya yi daga zargi daban-daban da aka masa a matsayinsa na shugaban bankin.
- Shugaban Kasa Muhamadu Buhari ya yi taro da gwamnonin APC ta intanet.
- Ministan Labaru Lai Mohammed ya ce sabanin tunanin PDP, gwamnati na samun nasarar yaki da rashawa tunda zuwa yanzun ta kwato fiye da naira biliyan dari takwas da wasu rikakkun gafiyoyin kasar nan suka wawura.
- Gwamnatin Tarayya ta ce akwai wasu kudade dala miliyan dari biyu da kasar nan ke sa ran samun su daga kasar Nezalan da Siwizalan na ribar man Malabu wato Malabu Oil Proceeds.
- Majalisar Wakilai ta ce dole sai Akpabio ya wallafa sunayen ‘yan majalisun da ya ce su ke kwangilolin raya yankin Neja Delta.
- Kwamitin da ke binciken Ibrahim Magu ya sanya talata mai zuwa a matsayin ranar ci gaba da binciken nasa.
- Buratai ya ce tsaro ya inganta a kasar nan idan aka kwatanta da shekaru biyar baya da suka gabata.
- Sojoji sun kashe ‘yan bindiga biyu suka kuma kama wani dan Nijar da ke yi wa ‘yan bindiga fataucin makamai a Katsina.
- A dalilan da Yakubu Dogara ya bayar na ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, har da zargin gwamnan jihar Bauci Bala Mohammed na karkatar da wani bashi naira biliyan hudu da rabi da ‘yan kai, inda gwamnan ya ce ba gaskiya a duk zargin da Dogara ya yi.
- Gwamnatin Tarayya ta kwato wata dala mliyan tamanin daga kamfanonin mai.
- Kotun daukaka kara ta yi fatali da karar da Dino Melaye ya daukaka a kan zaben Smart sanata na Kogi ta yamma, kotun ta ma umarci Dino ya biya Smart wata naira dubu hamsin saboda bata masa lokaci. Sai dai Dino ya ce bai hakura ba, zai kai gaba.
- An fitar da rahoton faduwar da jirgin sama mai saukar ungulu ya yi da Osinbanjo a ranar biyu ga watan Fabrairu na bara wato 2019, inda binciken ya nuna kuskure ne na dan Adam (Human Error) ya sa jirgin ya rikito.
- Gwamnatin jihar Kaduna ta kira wani taro na hukumomin tsaro don kawo karshen hare-hare, da ramuwar gaiya a kudancin jihar Kaduna.
- Wasu na cewa abin mamaki garin Zankuwa da ke kudancin jihar Kaduna, da a lokacin zaben Jonathan shekarar 2011 a watan Afrilu aka tarwatsa Hausawa da Fulanin garin, aka kashe na kashewa, aka raunata na raunatawa, aka sa ‘yan garin gudun hijira a sansanin Mando, Zankuwar ce ta zama wajen gudun hijira na kabilun yankunan da ake zargin Fulani sun tarwatsa na tarwatsawa, da kashe na kashewa da jikkata na jikkatawa a yanzun haka, har wani rahoto ke nuna suna korafin ba abinci ba kulawa a sansanin na Zankuwa. Shigen halin da Hausawa da Fulanin na Zankuwa suka kasance a wancan lokacin.
- Yanzun karfe uku na dare, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 624 a jihohi da alkalumma kamar haka:
Legas 212
Oyo 69
Neja 49
Kano 37
Oshun 37
Abuja 35
Filato 34
Gwambe 33
Edo 28
Inugu 28
Eboyi 17
Delta 10
Katsina 9
Ogun 8
Ribas 7
Ondo 5
Kaduna 4
Nasarawa 2
Jimillar da suka harbu 41,804
Jkmillar da suka warke 18,764
Jimillar da suka riga mu tafiya 868
Jimillar masu jinya 22,172
- Matar gwamnan jihar Binuwai da danta sun warke daga kwarona.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Jiya sai ga sako daga wani Ameen Ahmed kamar haka:
“Aslm, Dr inamaka fatan Alkhairi, hakika ina daya daga cikin masoyanka kuma ina bibiyarka kullum, inarokon Allah yakareka daga sharrin mutum da aljan, Allah yakareka daga sharrin duk wata halitta adoron kasa,
Wlh tun ina yaro banida burinda yawuce inzama Dan jarida amma Allah be yardaba, hakan baisamuba, nafara samun matsala ne tun daga iyaye saboda basuda kudinda zasu dauki nauyina domin cigaba da karatuna, haka inaji inagani karatun nawa yatsaya, sai daga baya Naje nakoyi sana ar hannu, har yakaiga Allah yataimakeni kuma na dogara dakaina, ayanzu nakai matsayinda ba karatunaba harna kannaina nadauki nauyimsu, kuma yanzu haka nasamu damar komawa karatu ina nan polytechnic main campus inda kake koyarwa, ina department din edu-tech ada, CTVE ayanzu, ina N.C.E 200lv to option dina shine wood work, saboda ni kafinta ne ayanzu, furniture, kuma ni haryanzu wannan burin nawa yananan domin haryanzu ina sha awar aikin jarida musamman yadda naga kanayi, Dr yanzu tambayata anan shine Dan Allah inada damarda zan iya karanta aikin jarida anan gaba? Kasancewar ni dalibin science ne, shin akwai matakinda zankai Wanda idan ina sha awar canzawa inkoma domin cikar burina? Ko kuwa babu, idan akwai Dan Allah inason Karin bayani dakuma shawarwari. Nagode kahuta lfy Allah yakarama rayuwar Dr Albarka”
Amsa: ina godiya kwarai da bibiya da so da kauna da addu’a. Ni ma ba aikin jarida na karanta ba, Hausa na karanta, kuma ban taba karatun aikin jarida ko samun wani horo ko na minti daya bangaren aikin jarida ba. Ga shi ina aikin da koyar da ‘yan jarida da sa ran nan gaba zan je in yi karatun na jarida. Da ke nuna cewa ba ka makara ba. Sauran karin bayani kana iya zuwa ofishina da ke rediyon sifaida a folin mu tattauna.
Ina kara godiya.
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi a DCL Hausa a :
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2662373640701697&id=2356865571252507
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.