Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, bakwai ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da takwas ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.
- A karshen taron da shugabannin kasashen yammacin Afirka ciki har da shugaban kasa Buhari suka yi, a kan rikicin kasar Mali ta hanyar intanet, sun yi kira ga shugaban kasar da ‘yan adawa su kafa gwamnati ta hada-ka a kasar.
- Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta umarci makarantun sakandare su bude daga hudu ga watan gobe, don dalibai da ke ajin karshe su koma, don shirya wa jarabawar fita ta WAEC da za a fara ranar goma sha bakwai ga watan na gobe.
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rada wa wasu tasoshin jiragen kasa na kasar nan sunayen Osinbanjo, da Tinubu, da Babatundo Fashola.
- Shugaban ‘Yan Sandan Kasar nan ya umarci kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, ya jogoranci tilasta aiki da dokar hana fita ko dare ko rana a kudancin jihar Kaduna, da kara wadata jami’an tsaro da kayan aiki.
- Gwamnatin Tarayya ta kara tsawon lokacin yin rajistar samun tallafin N-Power da mako biyu.
- Nijeriya na bin wasu kasashe uku dala biliyan tamanin da daya da rabi kudin wutar lantarkinta da suka sha ba su biyata ba.
- An kashe wani yaro, aka ji wa mutum biyar rauni a wani fada da aka yi a wajen hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar Neja.
- Kowa yana ci gaba da nasa hasashen a kan ficewar da Yakubu Dogara ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, sun soma tunanin anya za su ga dilin-dilin kafin Sallah kuwa ganin yau ashirin da takwas ba labari, ga sallar ta matso, kuma shekara daya da kusan wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi?
- Yanzun karfe uku na dare akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 648 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 180
Filato 148
Abuja 44
Ondo 42
Kwara 38
Ribas 32
Oyo 29
Kaduna 21
Oshun 20
Edo 17
Ogun 17
Kano 9
Binuwai 9
Delta 9
Abiya 9
Neja 7
Gwambe 3
Barno 1
Bauci 1
Imo 1
Jimillar da suka harbu 41,180
Jimillar da suka warke 18,203
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 860
Jimillar da ke jinya 22,117
- Jiya na zaga kasuwannin raguna da ke cikin garin Kaduna kama daga Zango ta Tudun Wadar Kaduna, zuwa kasuwar dabbobi ta Kawo, wacce za ka bi ta Unguwar Dosa ka bulle ta Kawo, ban ga kowa da takunkumi ko ana ba da tazara ko ruwan wanke hannu ba, kuma a cakude a ke. Wannan ya kawo ni ga batuna na AF na yau.
Af! Wasu ‘yan kasuwa da ke jihar Kaduna sun roke ni jiya in mika kukansu ta wannan dandali ga gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya taimaka ya bude musu kasuwanninsu da ya kulle. Domin kuwa sun ce sun shiga wani mawuyacin yali. Suka ce ga kasuwanni nan ana ci ko ina ba takunkumi, ba ba da tazara, ba batun sabulu na wanke hannu, kuma cutar kwarona kullum sai karuwa take ji a jihar Kaduna. Saboda haka suke rokon su ma a bude musu kasuwa su ci tasu kasuwar kamar kowa.
Za a iya leka rubutun labarun a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.