Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, shida ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da bakwai ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Ashe da Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila ya ba Ministan kula da raya yankin Neja Delta Akpabio sa’a arba’in da takwas ya wallafa sunayen ‘yan majalisar da Akpabio ya yi zargin su ake ba kwangilolin yankin Neja Delta suna yi, ko su dauki matakin shari’a a kansa, tabbas ya tattara sunayen ya mika wa majalisar amma shugaban majalisar ya ki karanta wannan sashen na sunayen, ya karanta wani abu daban don kare ‘yan majalisar daga jin kunya. Majalisar Matasan Nijeriya NYCN ce ta fasa wannan kwai ta gidajen rediyo da talabijin jiya, har ta nuna ainihin takardar sunayen da Akpabio ya mika, da ke kunshe da sunayen ‘yan majalisar, da kwangilolin, da ranakun, da sauransu amma Gbajabiamila ya ki karantawa a gaban majalisar. Duk in ji kungiyar ta matasa ta NYCN National Youth Council of Nigeria, ba in ji ni ba.
  2. Lauyan Ibrahim Magu ya ce sam sharri aka yi wa Magu da aka ce ya wawuri wasu kudade na kamfanin mai na kasa NNPC.
  3. Kungiyar kare bil’Adama da aka fi sani da SERAP a takaice, ta nemi Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da na Majalisar Wakilai Gbajabiamila su wallafa rahotannin binciken rashawa da ke hannunsu.
  4. Gwamnatin Tarayya ta bude tashoshin jiragen sama guda goma sha hudu don zirga-zirga ta cikin gida.
  5. Mutane na ci gaba da korafi a kan sabon kudin hawa jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja ko Abuja zuwa Kaduna da aka ce a yanzun ya koma a kalla naira dubu uku.
  6. ‘Yan Nijeriya su talatin da biyar aka kwaso daga Faransa da sauran kasashen Turai aka kawo su Abuja.
  7. Wata uwa da ‘ya’yanta hudu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon wata ambaliya a Gwagwalada Abuja.
  8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi, ga dilin-dilin ma an soma biyan wasu, su nasu sun ji shiru.
  9. Yau cutar kwaronabairos ke cika wata biyar da bayyana a kasar nan.
  10. Yanzun karfe hudu da minti biyu na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwarona su 555 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 156
Kano 65
Ogun 57
Filato 54
Oyo 53
Binuwai 43
Abuja 30
Ondo 18
Kaduna 16
Akwa Ibom 13
Gwambe 13
Ribas 12
Ekiti 9
Oshun 8
Kuros Ribas 3
Barno 2
Edo 2
Bayelsa 1

Jimillar da suka harbu 40,532
Jimillar da suka warke 17,374
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 858
Jimillar da suke jinya 22,300

Mu wayi gari lafiya.

Af! Kamar yadda na ambata kwanakin baya cewa limamin masallacin juma’a na Barnawa da ke cikin garin Kaduna da ke bibiyata kullum da asubah, yake kuma sa ni a cikin addu’a musamman idan yana hudubar sallar Juma’a, haka jiya labari ya ishe ni har gida cewa babban limamin masallacin juma’a na kwalejin foliteknik ta gwamnatin tarayya ta Kaduna Malam Abubakar Sadiq, ya ambato ni a hudubarsa ta sallar Juma’ar da ta gabata tare da mun addu’a. AMIN kuma su wadanan limamai, da sauran dinbin limamai da jama’a da ke mun addu’a a kullum, duk ina godiya Allah Ya ci gaba da kare mu gabadaya, Ya mana katangar karfe da masharranta, mahassada, magibata, magulmata, makasa, makidinafa, ma’asaranta da sauran ma ma ma ma da ba su da dadin ji ko gani Amin.

Za a iya leka rubutun labarun nawa na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply