Assalamu alaikum barkanmu da asubahin asabar, hudu ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyar ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Wasu daga cikin ma’aikatan gwamnatin tarayya sun soma jin dilin-dilin jiya bayan la’asar.
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Nijeriya daga tafiyar da ya yi Bamako ta kasar Mali.
- Tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ya kuma ficewa daga jam’iyyar PDP ya koma APC.
- Babban mai tsawatarwa na majalisar wakilai Tahir Munguno ya bai wa bangaren zartaswa shawarar ya dauki shawarar da Majalisar Dattawa ta ba shi ta ya kori manyan shugabannin tsaron kasar nan.
- Shugaban cocin Angilikan na kasa Arcibishof Buba Lamido, ya ba shugaban kasa shawarar ya duba shawarar da Majalisar Dattawa ta ba shi ta ya kori manyan shugabannin tsaron kasar nan saboda matsalar tsaro da ta addabi arewacin kasar nan.
- ‘Yan PDP da ke majalisar dokoki ta jihar Kaduna, sun koka a kan tabarbarewar matsalar tsaro a kudancin jihar Kaduna.
- Yanzun karfe uku da minti hudu na dare ana ruwan sama a nan Kinkinau kuma ba su dauke wuta ba. Af! Sun dauketa yanzun nan.
- Sojoji sun kashe ‘yan bindiga goma sha bakwai, a jihar Katsina, sai dai an kashe musu soja uku.
- Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka daga shugabancin kasar nan saboda ya gaza bangaren tsaro.
- Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce suna daukar matakan ganin masu kiba sun rage ta, ciki har da hana tallar abinci da abin sha da ke sa kiba a talabijin kafin karfe tara na dare, da kuma intanet.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata hudu ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi.
- Zuwa karfe uku da kusan rabi na dare da nake wannan rubutu akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 591 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Oyo 191
Legas 168
Abuja 61
Ondo 29
Oshun 26
Ebonyi 24
Edo 23
Ogun 14
Ribas 13
Akwa Ibom 12
Kaduna 10
Katsina 6
Barno 4
Ekiti 3
Delta 3
Imo 3
Neja 1
Jimillar da suka harbu 39,539
Jimillar da suka warke 16,559
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 845
Jimillar da ke jinya 22,135
- Kotu ta nemi Diezani ta dawo gida Nijeriya don mata shari’a a kan kudaden da ake zargin ta wawura ta tsallake.
- Hukumomin sojan sama, sun mika wa ‘yan sanda wadanda wajen yin ribas suka buge Tolulope ta riga mu gidan gaskiya.
Mu wayi gari lafiya.
Af! A ranar 25 ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da goma sha biyar 25/7/2015 wato yau shekara biyar daidai, na yi wannan rubutun da ke biye a dandalina na fesbuk da nake rubutu duk asubah:
‘Ni dai bacin kada jama’a su ce na cika azarbabi ba ko, da na ba Baba Buhari shawarar ya tsige su Burutai wato manyan hafsoshin soja na tsaron kasar nan ya nada wasu sababbi. Saboda da alamu su ma su Burutai irin su Alex Badeh da Mimimah ne ba za su iya yakar kungiyar boko haram ba. Amma fa ra’ayina ne. Ni da a ce soja ne da tuni na yi kundinbala na yi biji-biji da masu kashe bayin Allah’
Za a iya leka rubutun labarun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.