Assalami alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, uku ga watan Zulhijja, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin anabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da hudu ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Bamako ta kasar Mali in da zai tarar da wasu shugabanin kasashen yammacin Afirka guda biyar don gano bakin zaren warware takaddamar siyasa da ta yi wa kasar ta Mali dabaibayi. Sai dai an ta tsegumin karon farko an ga shugaban kasa Muhammadu Buhari sanye da takunkumi a lokacin da ya isa can Malin, da kuma wani tsegumin cewa karon farko da shugaban kasa ya taka ya fice kasar nan ke nan tun da kwaronabairos ya kunno kai a duniya. Wasu kuma ke korafin mai bunu a gindi ne ke kokarin kai gudunmawar kashe gobara.
- Majalisar Dattawa ta zargi kanta da kanta da gazawa wajen yin aikinta na sanya ido da bin diddigin ayyukan hukumar raya yankin Neja Delta, da har shugabanin hukumar suka samu damar wawurar dukiyar hukumar ba ‘yar kadan ba. Ita ma gwamnatin tarayya sun ce tana da nata laifin, tare da ba da shawarar a mayar da hukumar karkashin kulawar ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya don sanya mata ido sosai. Haka nan majalisar ta nemi a rushe shugabannin kwamitin rikon hukumar da tilasta su, su amayo wata naira biliyan biyar ba wasu ‘yan canji da suka yi kashe-mu-rabata.
- Yanzun karfe uku da rabi da wasu mintoci na goshin asubah ina wannan rubutu sauro na ta kawo mun farmaki saboda rabonmu da wutar lantarki tun jiya da sassafe. Shi ya sa za a ga labarun na yau ma ba yawa.
- Majalisar Wakilai na shirin kai ministan kula da al’amuran yankin Neja Delta Akpabio kotu saboda sa’a 48 da ta ba shi ya wallafa sunayen ‘yan majalisar da ya yi zargin su ne ake ba kwangilolin hukumar raya yankin, da kwangilolin da aka ba su, da kudaden da ranakun, ta wuce bai wallafa ba. Daga bisani ya aike wa majalisar takardar cewa shi bai yi wannan zargi ba, in ma akwai sunayen sirri ne aka ba shi da amanar ba zai fallasa ba. Majalisar ta ce za ta yi nazarin wasikar da ya aike mata da yanke shawara a kan matakin da za ta dauka na gaba.
- An bisne gawar Tololupe matukiyar jirgin sama na yaki da ‘yan ajinsu da suka taba yin karatu tare suka bugeta da ribas, ta riga mu gidan gaskiya. An bisneta ne a Abuja har marada ke cewa sun ga gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya halarci bisnewar ba takunkumi.
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki ta jihar Neja ya sauka daga mukaminsa ba tare da bayyana dalili ba, har an ma nada sabo.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i, duk na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata hudu ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi.
- Majalisar Wakilai ta nemi shugaban kasa ya mayar da shugabannin asusun nan na tallafawa na NSITF saboda an rusa su ne ba bisa ka’idar dokar da ta kafa asusun ba.
- Wasu mata sun yi zanga-zanga a jihar Kaduna don nuna fushinsu a kan matsalar tsaro da ta addabi jihar.
- Yanzun karfe hudu da minti goma na asubah, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 604 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 203
Oyo 87
Abuja 79
Edo 41
Osun 35
Ogun 24
Ribas 22
Kaduna 22
Akwa Ibom 20
Filato 18
Delta 9
Ebonyi 9
Imo 8
Inugu 5
Kano 5
Kuros Ribas 5
Katsina 4
Nasarawa 3
Barno 2
Ekiti 2
Bauci 1
Jimillar wadanda suka harbu 38,948
Jimillar wadanda suka warke 16,061
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 833
Wadanda ke jinya 22,054
- A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe don duba shafukana da ke dauke da rubutun labarun da na yi daga juma’ar da ta gabata, zuwa jiya alhamis.
Mu wayi gari lafiya, mu yi juma’a lafiya.
Af ! Jiya wata baiwar Allah ta turo mun wannan sakon:
“Assalamu Alaikum. Dr. Kusan ko da yaushe in na karanta rubutun ka nakan yi tunani cewar wannan dama ce, da za’a iya amfani da ita wajen jawo hankalin jihar kaduna. Ko ka san akwai list da gwabntin jihar kaduna ta yi Wacce ta Kira liability list Tun 2015? Na masu fansho da garatuti, ama har yanzu ba su biya mutane ba. Sai mutuwa masu shi ke yi. Pls in zai yiwu Kai kokari ka rika sakawa cikin rubutun ka kullum. Zaka Sami lada. Wallahi mutane na cikin wani hali. Ma’assalam”
To roke ni kada in bayyana sunanta.
Za a iya leka rubutun labarun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.