Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, biyu ga watan Zulhaj, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da uku ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Yau shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi Bamako ta kasar Mali, haka nan shugabannin kasashen yammacin Afirka biyar za su je Malin su ma duk a yau don haduwa su gano bakin zaren warware takaddamar shugabancin kasar tsakanin abokan hamayya da shugaban kasar.
  2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartaswa da aka saba yi duk mako. Su Osinbanjo da Boss Mustapha da sauran manyan mukarraban gwamnati sun halarta.
  3. A kudin da Nijeriya ta yi hasashen za ta samu a watanni uku na farkon shekarar nan, kudin ba su kai ba da gibin naira tiriliyan daya da kusan rabi wato 1.46 Trillion Naira deficit.
  4. Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta ba Nijeriya gudunmawar dala miliyan daya don ta yaki cutar kwarona da kudin.
  5. Cikin watanni shida da suka gabata hukumar kwastam da ke jihar Kwara ta tara naira bilyan biyu da kusan rabi ba ‘yan canji.
  6. Majalisar Dattawa ta amince da sunayen jakadu arba’in da shugaban kasa ya mika sunayensu.
  7. Kungiyar Boko Haram ta kashe wasu ma’aikatan agaji su biyar da suka yi wata daya a hannun kungiyar bayan ‘yan kungiyar sun kama su a wani samame da suka kai Mangonu da ke jihar Barno a watan jiya.
  8. Magu ya sake gurfana a gaban kwamitin da ke masa tambayoyi.
  9. ‘Yan sandan jihar Kaduna sun kama mutum 217 da suke zargi da kai hare-hare da kidinafin da sauran laifuka, biyo bayan samar da karin ‘yan sanda su dari biyar saboda yadda matsalar tsaro ke addabar mutanen jihar Kaduna.
  10. Ba a samu damar ci gaba da shari’ar mutum biyar da ake zargi da fashi a banki a Offa da ke jihar Kwara ba, saboda matsala ta kwaronabairos da ta hana ma’aikatan shari’a zuwa kotun.
  11. Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya harbu da kwaronabairos. Na jihar Ondo Ikpeazua ya warke.
  12. Gwamnatin jihar Kano ta ce ta hana shagulgulan Sallah amma za a yi sallar Idi ta hanyar kiyayewa da ka’idojin hana yada kwaronabairos.
  13. Mutum miliyan goma sha biyar ya harbu da kwaronabairos a duniya bakidaya.
  14. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya ke nan da kusan wata hudu suna dakon ariyas na sabon albashi.
  15. Karfe uku na dare da nake wannan rubutu, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 543 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 180
Abuja 86
Kaduna 56
Edo 40
Ondo 37
Kwara 35
Ogun 19
Ribas 19
Kano 17
Ebonyi 16
Inugu 16
Delta 7
Bayelsa 4
Bauci 3
Abiya 1

Jimillar wadanda suka harbu 38,344
Jimillar wadanda suka warke 15,815
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 813
Wadanda ke jinya 21,716

Mu wayi gari lafiya.

Af! Hukumar shirya jarabawa ta shiga manyan makarantu JAMB ta ba da umarni ga makarantu su soma daukar dalibai a watan gobe. Sai dai ta manta cewa daliban da aka dauka bara ba su matsa aji na gaba ba, ballantana a samu gurbin daukar sabbi saboda yajin aiki da kuma kwaronabairos. Jami’ar jihar Kaduna KASU ce kadai na san al’amuran karatunta na tafiya daidai ta hanyar koyar da dalibanta ta kafar intanet, saboda malaman ba su shiga yajin aikin ba. Ita tana iya daukar sabbin dalibai, amma sauran jami’o’i da manyan makarantun da ko dai yajin aikin ya hana koyar da daliban da ake da su a hannu ko har yanzun ba su soma koyar da dalibansu ta intanet kamar yadda KASU ta yi ba fa?

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply