Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkamu da asubahin laraba, daya ga watan Zulhaj, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyu ga watan Yuli, shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. Jiya aka yi jana’izar dattijo Ismaila Isa Funtuwa a Abuja da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwatanta da babban rashi a gare shi, shi kansa da kasa da duniya bakidaya, da addu’ar Allah Ya jikansa da rahama.
  2. Gwamnatin Tarayya ta ce babu gaskiya a raderadin da ake yi cewa ta kara wa ma’aikata da ya kamata su yi ritaya lokacin yin ritayar.
  3. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaban kasa Jonatha a kan aikensa da ya yi kasar Mali don wanzar da zaman lafiya.
  4. Majalisar Dattawa ta nemi manyan shugabannin tsaro na kasar nan su jirga gefe guda su ba da wuri saboda sun gaza samar da tsaro. Sai dai shugaban kasa ya ce a duk duniyar nan shi kadai ne yake da ikon nada shugabannin tsaro ko korarsu ko umartarsu su jirga.
  5. Majalisar Wakilai ta ba ministan yankin Neja Delta Akpabio sa’a arba’in da takwas ya wallafa sunayen ‘yan majalisar da ya yi zargin su ne ke gudanar da yawancin kwangolin da ake bayarwa na raya yankin Neja Delta, da irin kwangilar, da kudin kwangilar, da ranar da aka ba da kwangilar, in ba haka ba su sanya kafar wando guda da shi.
  6. Zuwa yanzun ‘yan Nijeriya dubu shida, da dari uku da goma sha bakwai aka dawo da su gida Nijeriya daga kasashen ketare.
  7. Kamfanin mai na kasa NNPC da kamfanin mai na Nijar sun sabunta yarjejeniyar Nijar ta ci gaba da sayarwa da Nijeriya tataccen man fetur domin biyan bukatun man a cikin gida Nijeriya, da aka dakatar da shigo da man daga Nijar zuwa Nijeriya saboda rufe kan iyakoki da Nijeriya ta yi watannin baya.
  8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da kusan wata hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  9. A al’umar Gora Goni da ke yankin karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna, wasu sun kai hari suka kashe mutum goma sha daya, suka ji wa mutum a kalla goma sha shida rauni, mutanen yankin sun tsere kauyuka mafi kusa irin su Zankuwa gudun hijira.
  10. Zuwa karfe uku na dare da nake wannan rubutu akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 576 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 88
Kwara 87
Abuja 82
Filato 62
Ondo 39
Inugu 28
Oyo 26
Taraba 24
Kaduna 20
Ebonyi 20
Edo 17
Kuros Ribas 16
Kano 14
Ribas 11
Ogun 10
Delta 9
Nasarawa 8
Oshun 8
Katsina 3
Imo 2
Kabbi 1
Barno 1

Jimillar wadanda suka harbu 37,801
Jimillar wadanda suka warke 15,677
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 805
Wadanda suke jinya 21,319

Mu wayi gari lafiya.

I. Af! Na ga wata takardar notis na yawo a soshiyal midiya cewa gwamnatin jihar Kaduna ce ta ba masu sayar da raguna a gefen hanya da wasu wurare da aka saba cin kasuwar raguna na wucin-gadi a lokaci irin wannan cewa ba a son ganin kowa a irin wadannan wurare.

Ii Hoton da ke biye ga wadanda suke iya ganin hoto a rubutuna, na hagu lokacin da nake horas da ma’aikatan gidan rediyon Nagarta ne, na dama kuma lokacin da nake horas da ma’aikatan gidan rediyon freedom/firidon ne.

Sauran gidajen rediyo da talabijin da na horas musu da ma’aikatansu sun hada da:

Rediyon Nijeriya na Kaduna
Rediyon jihar Kaduna
Rediyon jami’ar jihar Kaduna
Gidan Talabijin na Kasa NTA
Rediyo da Talabijn na Libati/Liberty
Rediyo da Talabijin na DITV da Alheri
Gidajen rediyo da talabijin karkashin makarantar Kaduna Media Academy
Ma’aikatan NewAge Network

Da sauransu.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply