Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, ashirin da tara ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hiirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.AW. Daidai da ashirin da daya ga watan Yuli na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Babban Hafsan Hafsoshin Mayakan Kasa na Kasar nan Tukur Buratai ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari karin haske a kan halin da ake ciki bangaren tsaro.
- Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Dalta NDDC Farfesa Daniel ya yi wata ‘yar gajerar suma a lokacin da yake ba da bahasi a gaban kwamitin binciken wawurar kudi da ake zargin an yi a hukumar.
- Ministan Yankin Neja Delta Akpabio ya ce ‘yan majalisar dokoki ta tarayya ake ba yawancin kwangilolin da ake bayarwa a yankin suna yi.
- Wasu kidinafas sun sace diyar wani dan majalisar dokoki ta jihar Kano da kuma wani dan uwansa.
- Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum a kalla goma sha takwas, wata ruwayar ke cewa mutum ashirin da daya suka kashe, suka ji wa kusan talatin rauni, a yankin karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.
- ‘Yan tireda da ke zaune kewaye da kasuwar Sabon Gari da kuma karkashin gada da gwammatin jihar Kano ta yi wa rusau sun yi zanga-zangar rashin amincewarsu.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata kusan na hudu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
- Shugaban Majalisar Dokoki ta jihar Binuwai ya harbu da kwaronabairos.
- Jami’ar Oxford ta yi nasarar hada maganin da ke iya yakar kwaronabairos, ya mata bijibiji sai buzunta a jikin dan Adam.
- Zuwa karfe uku na dare da nake wannan rubutu, akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 562 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Abuja 102
Legas 100
Filato 52
Kwara 50
Abiya 47
Kaduna 35
Binuwai 34
Oyo 26
Ebonyi 24
Kano 16
Neja 15
Anambara 14
Gwambe 12
Edo 11
Ribas 6
Nasarawa 5
Delta 5
Barno 3
Inugu 2
Bauci 2
Kabbi 1
Jimillar wadanda suka harbu 37,225
Jimillar wadanda suka warke 15,333
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 801
Wadanda ke jinya 21,091
Mu wayi gari lafiya.
Af! Da yake jiya na leka kauyenmu Guibi da ke yankin Karamar Hukumar Kudan ta jihar Kaduna, kamar kwanakin baya da na ba da rahoto, da kyar na iya kurdawa da motata na shiga kauyen, da kyar na iya kurdawa na fito saboda babu gada kamar yadda hotunan da ke biye da wannan bayani ke nunawa. Mun je ne tare da abokina Dafta Aliyu Ammani. Ga wadanda ba sa iya ganin hotunan lalacewar gadar, na iya leka dandalina na fesbuk mai sunan Ishaq Idris Guibi Guibi.
Za a iya leka rubutun labarun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.