Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Asabar goma sha biyu ga watan Rabi-ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da takwas ga watan Nuwamba, na 2020.

  1. Gwamnatin Tarayya da kungiyar malaman Jami’a ASUU, sun ci gaba da tattaunawa, sun ma cimma matsaya har shugabannin malaman, sun koma su sanar da sauran ‘ya’yan kungiyar yadda suka yi da Gwamnatin Tarayya, wanda daga nan ne ake sa ran malaman su hakura su janye yajin aikin.
  2. An ci gaba da tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya da shugabannin kungiyoyin kwadago a kan karin kudin mai da na lantarki. Kungiyoyin sun yi tsayin gwamin jaki dole sai Gwamnatin Tarayya ta janye karin da ta yi na farashin mai.
  3. Gwamnatin Tarayya ta ce za ta hukunta kamfanonin sadarwa da har yanzun suka kyale ake ci gaba da amfani da layukansu marasa rajista.
  4. Shugaban ‘Yan sandan Nijeriya ya yi gargadin ba za su yarda wasu su ci gaba da zanga-zangar lumana da ta rikide ta zama ta tashin hankali ba.
  5. Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da belin Sanata Ndume, da sharadin karbe fasfonsa, da gabatar da wani mutum da zai tsaya masa, mazaunin Abuja, da ke da gida a Abuja. Da ma Sanatan ya kalubalanci wannan tsarewa da kotu ta masa a kotun daukaka kara.
  6. An kama mutum tara da ake zargi da kashe shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa.
  7. An tarkato ‘Yan Nijeriya da ke Jamus, cikinsu har da wadanda suka ci zarafin Sanata Ekweremadu a can Jamus zuwa gida.
  8. Sarkin Musulmi ya ce a yanzun dai Arewa ce mafi rashin jin dadin zama a fadin kasar nan saboda matsalar tsaro da ta yi kaka-gida a Arewa.
  9. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi, da na Jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  10. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 246 a jihohi da alkaluma kamar haka:
    Legas 81
    Abuja 73
    Filato 39
    Kaduna 25
    Ogun 13
    Bauci 5
    Ribas 4
    Ekiti 2
    Taraba 2
    Kano 2

Jimillar da suka harbu 67,220
Jimillar da suka warke 62,686
Jimillar da ke jinya 3,363
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,171.

  1. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’dinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  2. Gwamnatin Tarayya ta kammala cika sharuddan ciyo/wo wani bashi na Dala biliyan daya da rabi.

Mu wayi gari lafiya.

Af!

Allah Ya kare mu daga kidinafas Amin.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya

Labarai Makamanta

Leave a Reply