Assalama alaikum barkanmu da asubahin Litinin, bakwai ga watan Rabi’ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhaammad S.A.W. Daidai da ashirin da uku ga watan Nuwamba, shekarar 2020.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 155 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 60
Katsina 37
Kaduna 35
Abuja 6
Ogun 4
Edo 3
Kwara 3
Ribas 2
Kano 2
Jigawa 1
Oyo 1
Taraba 1
Jimillar da suka harbu 66,383
Jimillar da suka warke 62,076
Jimillar da ke jinya 3,144
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,163
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yaba da tura ‘yan sanda na musamman da Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Mohammed Adamu ya ce zai yi zuwa jihar Nasarawa don gano wadanda suka sace shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, daga bisani aka tsinci gawarsa da harbi biyu na bindiga.
- Kidinafas sun sako ‘ya’yanmu daliban jami’ar ABU Zariya da suka yi kidinafin su tara, bayan an biya kudi, daidai arzikin gidan yaro daidai cinikinsa. In kai dan talaka ne naira miliyan biyu, in dan mai hali ne har naira miliyan ashirin da biyar. Haka kowa aka biya nasa aka sako shi shekaranjiya wuraren karfe daya da wasu mintoci na dare.
- A yankin Rigasa da ke jihar Kaduna an kashe mutum uku a wani hari da kidinafas suka kai.
- Nijeriya da Nijar sun sanya hannu a wata yarjejeniya ta shigo da danyen mai kasar nan.
- Atiku Abubakar ya ce da an bi shawararsa da tattalin arzikin kasar nan bai kuma shiga mawuyacin halin da ya shiga a halin yanzun ba wato RECESSION.
- A jihar Zamfara gwamnan jihar Matawalle ya ce ya ceto mutum goma sha daya, maza goma mace daya da suka kwashe wata biyu zuwa uku a hannun kidinafas, sakamakon sasantawar da ya yi da kidinafas.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
- Ministan Kwadago Ngige ya ce su ba su tsame malaman jami’a daga tsarin IPPIS ba, sun dai ce ne a biya malaman da ba su shiga tsarin ba zuwa yanzun, albashin da suke bi na wata da watanni ta amfani da tsohon tsarin da ba na IPPIS ba.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Wata kotu ta yi fatali da wani korafin shugaban Amurka Donald Trump a kan kayen da ya sha a hannun shugaban Amurka mai jiran gado Biden.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Talakawa na korafin shi ke nan karin kudin mai ya zauna, karin kudin wuta ya zauna, karin kidinafin ya zauna, karin kashe-kashe ya zauna, karin kwaronabairos ya zauna, karin durkusher tattalin arzikin Nijeriya ya zauna, karin tsadar kayayyakin abinci da na abin masarufi ya ya ya ya ya ya ya ya zauna!
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
https://www.facebook.com/2356865571252507/posts/2764905293781864/
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.