Assalama alaikum barkanmu da asubahin Juma’ati babbar rana, hudu ga watan Rabi’ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin ga watan Nuwamba, shekarar 2020.
- Ministan Labaru Lai Mohammed ya ce Gwamnatin Tarayya, ba za ta rufe soshiyal midiya ba, amma za ta hada kai da wadanda lamarin ya shafa domin sanya ido. Ya kuma zargi CNN da fadin labarin da ba gaskiya ba na cewa sojoji sun yi kisan kare dangi ga masu zanga-zangar kiran kawo karshen ‘yan sandan SARS a Lekki da ke Legas, a ranar ashirin ga watan jiya. Har da batun za a sanya kafar wando guda da tashar ta CNN. Sai dai tashar ta CNN ta mayar wa da Lai Mohammed martanin babu karya a rahoton nata da ta bayar.
- A yau Juma’a ake sa ran Gwamnatin Tarayya da malaman jami’a da ke yajin aiki za su ci gaba da tattaunawa ko a samu su janye yajin aikin dalibai su samu su koma makaranta.
. - Masu motocin sufuri da ke bin hanyar Legas, da hanyar Abuja, da bin sauran titunan Arewa, sun yi barazanar janye motocinsu daga hanyoyin saboda matsalar kidinafin.
- A jihar Oyo an horas da jami’an tsaro na AMOTEKUN su dubu daya da dari biyar.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 144 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 62
Abuja 23
Kaduna 21
Ogun 12
Ribas 12
Ondo 5
Oyo 3
Filato 3
Bauci 2
Katsina 2
Kano 1
Jimillar da suka harbu 65,839
Jimillar da suka warke, 61,573
Jimillar da ke jinya 3,101
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,165
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin da alamu sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna ta musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Wutar lantarki ta ci gaba da tabarbarewa duk da karin kudin da aka mata. An kara wa talakan Nijeriya kudin zama a duhu, da karin kudin mai duk a zamanin Baba Buhari mai tausayin talakan Nijeriya.
- A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe, domin duba shafukana da ke dauke da rubutun labarun da na kawo muku, daga Juma’ar da ta gabata, zuwa jiya Alhamis.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Yau Juma’a sai mu dage da addu’a Allah Ya mana maganin kidinafas, da ‘yan siyasa ‘yan wala-wala da gwamnatin da ba talaka ne a gabanta ba.
Ia’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.