Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Gui?i

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Laraba, biyu ga watan Rabi’ul Sani, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha takwas ga watan Nuwamba, shekarar 2020.

  1. Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani Hakimi da dansa, a kauyen Gidan Zaki, da ke yankin karamar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna.
  2. Kidinafas sun kashe mutum biyu, suka yi kidinafin mutane da dama a yankin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
  3. Kidinafas sun yi kisa a marabar Kajuru ta jihar Kaduna, suka yi kidinafin wasu.
  4. Kidinafas sun harbi mutun daya yana asibiti yana jinya, suka yi kidinafin wani malami, da kuma wasu yara biyu a kwalejin foliteknik ta Nuhu Bamalli da ke Zariya, jihar Kaduna.
  5. Kidinafas sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja, kusa da Katari ta jihar Kaduna, sun kashe mutum biyu suka yi daji da wasu, sai dai jami’an tsaro sun ce sun ceto su, amma jami’ar ABU na cewa an yi kidinafin dalibanta a hanyar su goma sha, har yanzun shiru.
  6. Makasa sun je Kauyen Albasu da ke Sabon Birni a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, suka kashe mutum goma sha biyu.
  7. Makasa sun je yankin Ikara ta jihar Kaduna, sun kashe wani Mai Gari suka yi tafiyarsu.
  8. Kidinafas sun je Rigachikun ta jihar Kaduna, suka kashe wata mai juna biyu, suka yi kidinafin mijinta.
  9. Makasa sun je Kidandan da ke yankin Giwa ta jihar Kaduna, suka kashe mutane rututu kuma har yau ba su kyale su ba.
  10. Al’umomi da ke kusa da tashar jiragen sama ta Kaduna, da na kusa da kwalejin horas da kananan hafsoshin soja NDA sun ce nan wuraren kidinafas suka fi sakata su wala.
  11. Masu motocin sufuri zuwa Birnin Gwari sun ce hanyar ta zama tarkon kidinafas.
  12. Mutanen yankin Sabon Garin Zariya da ke jihar Kaduna, sun ce kauyakunsu sun zama tungar barayin shanu.
  13. Mutanen Mando da wuraren aisanta da ke cikin garin Kaduna, su ma sun ce da ido daya suke bacci.
  14. Daga Kudan ma ta jihar Kaduna, labari ne na an yi kidinafin wasu mutanen garin.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Yau kuwa aka ce za a fara kamen masu motoci da takardunsu suka kare aiki, ko lasisinsu ya kare aiki, ko suke amfani da tsohuwar lamba a jihar Kaduna.

Ni dai ina da komai amma lambata tsohuwa ce. Idan kun ji an yi ram da ni to lamba ce. Ga ta da dan karen tsada. Amma harajin nan na naira dubu daya da kowanne baligi da ke jihar Kaduna zai soma biya, sai watan jibi tukuna.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://www.facebook.com/2356865571252507/posts/2760928524179541/

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Related posts

Leave a Comment