Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, ashirin da takwas ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin ga watan Yuli shekarar dubu biyu da ashirin.

 1. ‘Yan Nijeriya dari da hamsin da shida aka kwaso jiya daga Sudan, da Faransa, da Ingila, da Kanada, da Jamus da sauran wasu kasashe.
 2. Ministan kula da al’amuran wajen kasar nan Geoffrey Onyeama ya harbu da kwaronabairos.
  Shugaban Majalisar Dokoki ta jihar Binuwai ma ya harbu.
 3. An raba naira biliyan dari shida da hamsin da daya da ‘yan kai na watan Yuni tsakanin gwamnatin tarayya, da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da idan an yi sa’a ma’aikata su ji dilin-dilin kafin Sallah.
 4. Dakarun soja sun murkushe wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram da ISWAP da ya yi kokarin tsallaka kan iyaka zuwa Kamaru. Wata ruwayar ke cewa kwamandoji shida sojojin suka kashe.
 5. A al’umar Janruwa da ke jihar Kaduna. Kidinafas sun je da karfin bindiga wasu ma ta taga suka dinga janyo su, suka yi awon gaba da wata ‘yar sanda, da diyarta, da wasu mutum hudu.
 6. Kungiyar SERAP ta kare hakkin bil’Adama ta nemi shugaban kasa ya dakatar da ministan Neja Delta Akpabio.
 7. Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i da sauran manyan makarantu JAMB ta sanya 21 ga watan gobe a matsayin sabuwar ranar da jami’o’i da sauran makarantu za su dauki sabbin dalibai na shekarar dubu biyu da ashirin.
 8. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata na hudu ke nan suna jiran ariyas na sabon albashi.
 9. A duniya bakidaya mutum miliyan goma sha hudu ya harbu da kwaronabairos.
 10. Da wuraren karfe uku na dare da nake wannan rubutu mutane 556 suka harbu da kwarona a Nijeriya a jihohi kamar haka:

Edo 104
Legas 97
Abuja 70
Binuwai 66
Oyo 61
Kaduna 38
Filato 28
Oshun 19
Akwa Ibom 14
Ribas 13
Katsina 13
Ondo 13
Ogun 6
Kano 5
Nasarawa 4
Gwambe 2
Ekiti 2
Barno 1

Jimillar wadanda suka harbu 36,663
Jimillar wadanda suka warke 15,105
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 789
Wadanda ke jinya 20,769

Mu wayi gari lafiya.

Af! Ina tunatar da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai cewa tsaro fa ba shi da lafiya a jihar Kaduna. Kashe-kashe da kidinafin kusan kullum.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Exit mobile version