Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, ashirin da bakwai ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.W.A. Daidai da goma sha tara ga watan Yuli na shekarar 2020.

  1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rada wa wata tashar jiragen kasa da ke jihar Delta sunan Goodluck Jonathan don martaba shi.
  2. Hukumomin sojan saman Nijeriya sun soma binciken ‘yan ajin su Tolulope mayakiyar sama ta Nijeriya da suka yi sanadiyyar mutuwarta wajen yin ribas, saboda an ma gano ba su da lasisin tuka mota.
  3. Kotu ta hana ‘yan sanda kama tsohuwar makaddasar shugaban hukumar raya yankin Neja Delta Joi da a yanzun haka gwamna Wike ya ba ta mafaka a gidan gwamnati bayan ya yi karfa-karfa ya hana ‘yan sanda kama ta.
  4. ‘Yan Nijeriya 324 aka kwaso jiya daga Amurka da wasu kasashen.
  5. Gwamnatin Tarayya da hukumar shirya jarabawar Yammacin Afirka WAEC sun amince su matsa da ranar soma jarabawar daga hudu ga watan gobe zuwa biyar ga watan jibi.
  6. Daga gobe litinin manyan sakatarori da daraktoci da shugabannin sassan gwamnati na jihar Kaduna za su soma zuwa aiki kullum, ma’aikata da ke matakj na goma sha hudu zuwa sama, ranakun litinin da laraba da juma’a, sai masu mataki na bakwai zuwa sha uku ranar talata da alhamis kadai.
  7. Wani abu da wasu ke cewa gurneti ne, wasu kuma ke cewa bam ne, ya yi sanadiyyar mutuwar wasu yara biyar da suke je gona yo ciyawa a wani kauye da ke yankin karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
  8. Wasu sun yi wa sojoji kwanton-bauna a Jibiya ta jihar Katsina, suka kashe sojoji biyu, suka yi wa fiye da sojoji ashirin rauni suna asibiti.
  9. A jihar Taraba an yi ba – ta – kashi tsakanin kidinafas da ‘yan banga, aka kashe ‘yan banga biyu aka ji wa hudu rauni.
  10. A yankin Kajuru da ke jihar Kaduna an kai sabon hari aka kashe mutum a kalla biyar.
  11. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata uku ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
  12. Yanzun karfe uku na dare akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 653 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 115
Kwara 86
Inugu 80
Abuja 78
Ribas 36
Ondo 35
Oyo 30
Katsina 28
Kaduna 19
Abiya 19
Nasarawa 18
Filato 17
Imo 16
Ogun 9
Ebonyi 9
Binuwai 9
Kano 9
Delta 8
Bauci 7
Ekiti 6
Gwambe 4
Bayelsa 4
Adamawa 4
Oshun 4
Kuros Ribas 1
Yobe 1
Barno 1
Zamfara 1

Jimillar wadanda suka harbu 36,107
Jimillar wadanda suka warke 14,938
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 778
Wadanda suke jinya 20,391

Mu wayi gari lafiya.

Af! Kada mu sake da addu’a Allah Ya raba mu da sharrin mutum da na karfe Amin.

Za a iya leka Taskar Guibin ta yau da ke DCL Hausa a :

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply