Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, ashirin da biyu ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da takwas ga watan Nuwamba, shekarar 2020.
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Joe Biden murnar nasarar lashe zaben shugaban kasa Amurka da ya yi. Da kira ga Biden ya lalubo hanyoyin hadin kai tsakanin Nijeriya da Amurka, da kuma tallafa wa kasashen Afirka. Ta dai tabbata Joe ya tika Trump da kasa. Joe na da kuri’a 273, Trump yana da 213. Joe zai zama shugaban Amurka na arba’in da shida.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 59 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Kaduna 28
Ribas 9
Ogun 8
Ondo 8
Kano 2
Neja 2
Kwara 1
Filato 1
Jimillar da suka harbu 63,790
Jimillar da suka warke 59,884
Jimillar da ke jinya 2,752
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,154
- Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya, ya amince wa ‘yan sanda su yi amfani da hanyoyin da suka wajaba, da ba su saba wa doka ba, wajen kare kansu, da iyalansu da dukiyoyinsu, da jama’a, da dukiyoyin jama’a, da na gwamnati ga duk wani dan ta da zaune tsaye.
- Hukumomin soja, sun gabatar da wata rantsuwa ga kwamitin da ke bincike a Legas da ke cewa, sun yi amfani da BLANK BULLET ne wajen DISPERSING masu zanga-zangar #ENDSARS da suka yi cincirindo a Lekki ta Legas. (Ni na yi wannan ENGAUSAR ba su ba).
- Kidinafas na ci gaba da yi wa al’umar Kidandan da ke yankin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna dauki-daidai, da dauki-bibbiyu, da dauki uku-uku a yankin.
- Wasu bayanai na nuna Gwamnatin Tarayya na barazanar kai kungiyar malaman jami’a kotu. Har zuwa yau an kasa daidaitawa tsakanin gwamnatin da malaman. Duk da ta rike musu albashi na wata da watanni su kuma ko a jikinsu.
- Idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, za su cika shekara biyu, suna zaman dakon ariyas na sabon albashi.
- Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa, bai gyara musu ba.
- Gwamna Zulum na jihar Barno, ya jajanta wa Gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas, abin da ya auku a jihar ta Legas.
Mu wayi gari lafiya.
Af! Ga wadanda suke iya ganin hotunan da ke biye da wannan rubutu, hotuna ne na wasu daga cikin kayan aikinmu a kamfanin Guibi-Hausa Services, da aka yi wa rajista da hukumar yi wa kamfanoni rajista ta kasa CAC, tun shekarar 2012 wato shekara takwas ke nan. Wannan kamfani ne ke horar da ma’aikatan rediyo da talabijin da jarida, da fassara da sauran aikace-aikace, daga ciki da wajen Nijeriya.
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.