Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Gui?i

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Talata, goma sha bakwai ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da uku ga watan Nuwamba, shekarar 2020.

  1. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 72 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 57
Abuja 6
Ogun 4
Kaduna 3
Neja 2
Ondo 2
Filato 2
Katsina 1
Oyo 1

Jimillar da suka harbu 63,036
Jimillar da suka warke 59,328
Jimillar da ke jinya 2,561
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,147

  1. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  2. Jiya ilahirin gwamnonin jihohin Arewa, da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, da Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, da Ministoci, da Shugaban ‘Yan sandan Nijeriya, da kusoshi bangaren tsaro, da Sarakuna na duk na Arewa, sun yi dafifi a nan Kaduna, don gano bakin zaren hana al’adar #ENDSARS ta samu gindin zama a zukatan mutanen Arewa, da batun tsaro, da gudunmawar da Sarakuna za su ba da, da jinjina wa malamai magadan Annabawa saboda kokarin da suka yi bangaren hana zanga-zangar yin tasirin a zo a gani a Arewa.
  3. Kungiyoyin kare hakkin al’umar Musulmi sun soma korafi, a kan yadda ake yi wa ‘yan Arewa da Musulmi kisan wulakanci, da kona masallatai ko rushe su, da sanyawa dukiyoyinsu wuta a jihohin Inyamurai. Na baya-bayan nan shi ne na Nsukka.
  4. ‘Yan Boko Haram sun kai hari kusa da Chibok, suka kashe mutum a kalla goma sha biyar, da kona gidaje masu yawan gaske.
  5. Daga daya ga watan nan an kara kudin wuta. Kafin karin idan na ba da naira dubu daya ana ba ni awo 36 da ‘yan kai. Ranar da aka yi karin na sayo kati na dubu daya, aka ba ni awo 30 da ‘yan.
  6. A watan Yuli, da Agusta da Satumba na shekarar nan, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira Biliyan 424 da ‘yan kai, harajin tamanin kaya wato VAT. Da ke nuna an samu karin kashi 54 da rabi da ‘yan kai.
  7. Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa kamfanonin jiragen sama da Naira Biliyan Hudu wato BAIL OUT.
  8. Hukumar EFCC na nan tana bincikar tsohon shugaban Hkumar Tara Kudaden Shiga na Cikin Gida FIRS Fowler saboda zargin ya yi wata damfara ta Naira Biliyan Biyar. Haka nan ECFF ta sake gurfanar da tsohon gwamnan Binuwai kuma Sanata a yanzun, Suswan saboda zargin ya wawuri wata Naira Biliyan 3 da ‘yan kai.
  9. Hukumar Jarabawa ta Yammacin Afirka WAEC, ta fitar da sakamakon jarabawarta ta shekarar nan, inda ta rike sakamako guda dubu dari biyu da goma sha biyar, da dari da arba’in da tara. Saboda zargin magudi.
  10. ‘Yan sandan SWAT da suka maye gurbin na SARS, sun soma samun horo a jihar Nasarawa.
  11. ‘Yan sanda sun kwato karin wasu taraktoci guda 30 da masu wasoso suka wawushe a jihar Adamawa.
  12. Kwamitin Majalisar Wakilai ya bukaci Gwamnatin Tarayya, ta dan tsahirta da niyyarta ta jinginar da tasoshin jiragen sama hudu da ta ce za ta jinginar da su.
  13. Yara, na boko da Islamiyya da Hadda, da ba a dade da komawa ba, sun ce “baba an ce a kawo kudin makaranta” Abin ya zo in ji mai tsoron wanka.
  14. Idan Allah Ya kai mu watan Afrilu, na shekara mai zuwa, ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

Mu wayi gari lafiya.

Af!
A kamfanin Guibi-Hausa Services, bayan aikin horas da ma’aikatan rediyo da talabijin da jarida, yana kuma sana’ar fassara. Kamfanin ya fassara takardu bangaren siyasa, da kimiyya, da tattalin arziki, da bangaren lafiya, da zamantakewa, da jawabai, da littafai. Yana kuma duba Hausar littafi don taceta da tsarkaketa da sauransu.
In ana bukata sai a tintibi kamfanin a
Q.1. Layin Adamawa da ke Kinkinau Kaduna. Ko
08023703754.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2747183202220740&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Related posts

Leave a Comment