Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Litinin, goma sha shida ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyu ga watan Nuwamba, na shekarar 2020.
- Yau daukacin manyan makarantu na gaba da sakandare mallakar gwamnatin jihar Kaduna za su koma makaranta. Haka nan duk makarantu na firamare da na sakandare za su koma makaranta tara ga wannan watan.
- ‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargi sun yi wasoson kayayyaki a jihar Kaduna su casa”in da uku, wata ruwayar kuma ta ce mutum dari da hamsin da bakwai aka kama, har da wadanda suka kwashi kaya a ofishin shiyya na hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC.
- A jihar Katsina sojoji sun ceto mata uku masu shayarwa da goyonsu, sai dai sun kashe uku daga cikin ‘yan bindigan, su kuma suka kashe soja daya.
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa matasa goma sha biyar da suka nuna kwazo wajen kirkire-kirkire ciki har da wani dalibi na jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. An ba kowanne kyautar kudi da sauransu.
- Kungiyar kare hakkin bil’Adama ta SERAP da wasu kungiyoyi daban-daban har 261, sun kai Hukumar Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa NBC kara kotu, saboda cin gidajen talabijin na Channels, da AIT da sauransu tara.
- Lai Mohammed ya ziyarci tashar talabijin ta TVC da aka kona a lokacin zanga-zanga a Legas, inda ya ce abin da aka musu hari ne ga dimukradiyya da kuma ‘yancin fadin albarkacin baki.
- Gwamnatin Tarayya ta bude sabon dandali na intanet da ‘yan kasuwa kanana da matsakaita za su iya samun tallafinta.
- Gwamnatin jihar Legas ta dage duk wata doka ta hana walwala a jihar.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin an biya sauran ma’aikata albashin watan jiya su an manta da su. Sannan idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi, alhali an dade da biyan sauran ma’aikata. Sannan malaman jami’o’i akwai masu bin albashin wata da watanni.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 111 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 49
Abuja 30
Ribas 11
Filato 10
Ogun 4
Kaduna 3
Oshun 1
Jimillar da suka harbu 62,964
Jimillar da suka warke 58,790
Jimillar da ke jinya 3,028
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,146
- Hadiza Bala Usman ta ce motoci ashirin da bakwai masu zanga-zanga suka kona har da gine-gine a shalkwatar hukumar tashoshin jiragen ruwa da ke Legas. Ta ce sai dai duk abin da suka lalata yana da inshora.
- Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
Mu wayi gari lafiya don yanzun karfe hudu daidai na asubah, Ladan na kiran assalatu.
Af! A ranar daya ga watan Nuwamba, na shekarar 2014, jiya shekara shida daidai na yi wannan rubutu da zai biyo baya a kasa, bayan na sha da kyar, sakamakon shugabantar alkalai da na yi, a gasar mawakan Hausa mai suna ZAKARAN GWAJIN DAFI. Gasar da wasu suka shirya da hadin gwiwar rediyon Nijeriya Karama a Kofar Gamji wato Gamji Gate. Musbahu Ahmed ya yi na daya, Yaro Dan Hausa ya yi na biyu, Yaro mai Da’a ya yi na uku, Halima Dan Zaki marigaiya ta zo ta daya a mata. Kuma aka ba kowanne mota. Na ce na sha da kyar ne saboda ni na san me na gani kafin gasar, da lokacin gasar da aka kwana uku ana yi, da kuma bayan gasar har da watannin da suka biyo baya. Bayan wannan ne na yi wannan rubutu:
‘Da karfe goma na safiyar nan Dan Ajilo Danguzuri zai kaddamar da wasu wakokinsa a cibiyar mata da ke nan cikin garin Kaduna, inda aka gayyaci Kamfanin Guibi-Hausa Services ya gabatar da Makala a kan Waka da ka’idojinta. Sai a kasance a wajen don jin me Makalar ta kunsa’
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.