Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, goma sha biyu ga watan Rabi’ul Awwa, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da tara ga watan Oktoba, shekarar 2020.

  1. Yau take ranar Maulidi, ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal da aka haifi Annabi Muhammad S.A.W. Har Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun yau, domin shagulgulan na Maulidi.
  2. Gwamnatin jihar Kaduna ta cire dokar hana walwala a dukkan kananan hukumomi 23 da ke jihar. Dokar hana walwalar za ta dinga soma aiki ne daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe. Wato da zaran shida ta yamma ta yi, ba a son ganin kowa yana yawo a duka kananan hukumomin jihar Kaduna, har sai shida ta safe. Daga shida ta safe kowa na iya fita, sai karfe shida da yamma kowa ya san inda dare ya masa.
  3. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Nijeriya a daina kalaman da ka iya wargaza hadin kan kasar nan. Ya yi kiran ne a wajen kaddamar da tambarin tunawa da ‘yan mazan jiya na 2021 da suka kwanta dama
  4. Hukumomin sojan runduna ta tamanin da daya, ta ce gwamnatin jihar Legas ce ta nemi ta je ta tabbatar da dokar hana walwala da ta kafa sa’o’i kadan da kafar doka, amma ba ta kashe kowa a Lekki ta Legas kamar yadda ake zarginta da yi ba.
  5. Kungiyar kare hakkin bil’Adama ta Aminasti, ta bukaci lallai gwamnatin Nijeriya, ta daina wata rufa-rufa ta binciki sojojin da suka kashe masu zanga-zangar lumana a Lekki ta jihar Legas, domin kamar yadda kungiyar ta fada, tana da shaidar cewa sojoji ne suka yi kisan. Sojoji kuma kamar yadda suke ta bayani, sun ce kage aka musu.
  6. Okonjo Iweala ta zama mace ta farko ‘yar Afirka da za ta shugabanci hukumar kasuwanci ta duniya WTO a takaice.
  7. Idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.
  8. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  9. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 147 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 82
Abuja 20
Ribas 9
Kaduna 8
Filato 8
Binuwai 5
Edo 3
Kano 3
Nasarawa 3
Taraba 3
Ogun 2
Bauci 1

Jimillar da suka harbu 62,371
Jimillar da suka warke 58,095
Jimillar da ke jinya 3,137
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,139

Mu wayi gari lafiya.

Af! Jiya na leka Rediyon Nijeriya na Kaduna. Ikon Allah duk ofishin da na leka, muna zaune muna hira, sai wanda muke hirar da shi ya ce “Malam Guibi ga dilin-dilin muna hirar nan ya shigo”

Yanzun karfe hudu da minti hudu na asubah.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Labarai Makamanta