Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, shida ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da uku ga watan Oktoba, na shekarar 2020.
- Jiya da karfe bakwai na almuru shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa al’umar kasar nan jawabi ta gidajen rediyo da talabijin da sauran kafofi na intanet, bayan shawarar da ake ta ba shi musamman Majalisar Dattawa ta ya daure ya yi wa al’umar kasar nan jawabi saboda halin da ake ciki.
A jawabin na shugaban kasa Buhari, ya bukaci matasa su dakatar da zanga-zangar haka nan ta isa. Buhari ya ce shiru-shirun da yake yi ba fa tsoron wani yake ji ba, kuma kada a dauka shirun nasa gazawa ce. Ya kawo irin kokarin da gwamatinsa ke yi don ci gaban kasa da rage fatara, da sauransu.
Sai dai na ji wasu daga wadanda suka saurari jawabin na korafin babu komai a cikin jawabin da yake sabo a wajensu. Suka ce sun dauka za su ji ya ce ya kori wane da wane a gwamnatinsa musamman bangaren shugabannin tsaro. Sai suka yi shiru. - Mataimakin Shugaban Kasa Osinbanjo ya yi alkawarin za a yi adalci a kan kisan da ake zargin an yi a Lekki da ke Legas.
- Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya ba da umarnin janye ‘yan sanda da ke gadin wasu manya. Aka ce sai ka ga ‘yan sanda goma na gadin babban mutum shi daya tal tilo.
- Gwamnonin jihohin Arewa da kawancen kungiyoyin Arewa, sun ja hankalin matasan Arewa da su ci gaba da hakurin da suke yi, kada su ce za su yi ramuwar gaiya ga cin kashin da aka yi wa ‘yan Arewa da ke kasashen Inyamurai da Yarbawa a wannan zanga-zangar da ta rikide ta zama tashin hankali da fada, shigen na kabilanci da ake ta farma ‘yan Arewa da ke Kudu.
- Gwamnatin Tarayya ta bai wa asibitocinta na gwamnatin tarayya umarnin idan an kai musu wanda aka jikkata sakamakon zanga-zangar da ake yi, kada su bata lokaci wajen karbarsa da yi masa magani kyauta, ba sai sun jira ya biya ba.
- Babban Sakatare Janar na kungiyar kasashe renon Ingila, da kungiyar ECOWAS/EKOWAS sun yi kira ga masu zanga-zanga su gudanar da ita cikin ruwan sanyi.
- Hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO/NEKO ta matsa da jarabawarta da ta kamata a rubuta jiya da yau da gobe, sai ranar 17 da 18 da 19 ga watan gobe.
- Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna zaman dakon ariyas na sabon albashi.
- A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito an jima da safe, don duba shafukana da ke dauke da rubutun labarun da na kawo muku, daga Juma’ar da ta gabata zuwa jiya Alhamis.
Mu wayi gari lafiya, mu yi Juma’a lafiya.
Af!
A wadanda suka yi tsokaci a rubutuna na jiya, tsokacin wani Muhammad Lawal ne ya fi daukar hankalina kamar haka:
“Hmm ai zalumtar da aka shiryo don talauta Arewa da yi mata kisan kare dangi eh kare dangi Mana tunda kauye ne za azo a bude Mai wuta yaro da babba mata da maza duk aita kisa ba kakkautawa ai Kai kasan akwai manufa infa kun iya tunawa kafin su aukoma mutane Saida suka gama bin dabbobinmu da sata bayan sungama sace Mana dabbobinmu kaf, Sai suka koma kisan wayanda suka rage na dabbobin kafin sukawo kan Al’umma duk basuci masaran abinda suke nemaba suka koma kan akori jamian sojoji akaki kulasu yanzu Sai suka Sami kafa na SARS shine suka shiga zanga zangar da ba kare,to yanzu Kai kayi ya Fara komawa kan mashekiya ai, Allah Kara tona musu asiri Alfarman Annabi da Alkur’ani Amin”
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
https://www.facebook.com/2356865571252507/posts/2736919293247131/
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.