Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Alhamis, biyar ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyu ga watan Oktoba, shekarar 2020.
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kiran a yi hakuri tare da fahimtar kokarin da gwamnati ke kan yi don biyan bukatun masu zanga-zanga.
- Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya yi kira ga shugabannin al’uma su taimaka su sa baki don kwantar da tarzomar da matasa ke kan yi.
- Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar,, da Obasanjo, da Oni na Ife, da Gbajabiamila shugaban majalisar wakilai, da Tinubu, da Clinton,, da Hillary Clinton da sauran mashahuran shugabannin duniya, da mutane na ciki da wajen Nijeriya, sun nuna rashin jin dadinsu a kan kazancewar zanga-zangar lumanar #ENDSARS da kuma kisan da ake zargin jami’an tsaro sun yi wa matasan. Har Shek Dahiru Bauci ya ce ba a kashe wuta da wuta.
- Kungiyar kare hakkin bil’Adama ta amnasti da ta Human Right Watch sun zargi sojoji da kashe masu zanga-zanga su goma sha biyu, a Legas, zargin da sojoji suka kira FAKE NEWS.
- Fusatattun masu zanga-zanga da ke zargin jami’an tsaro sun bindige wasunsu a Lekki Plaza da ke Legas, sun banka wa ginin tashar TVC, da tashar talalabijin ta jihar Legas, da shalkwatar hukumar tashoshin jiragen ruwa, da shalkwatar hukumar kiyaye hadurra ta kasa wuta. Suka kuma kai hari gidan Oba na Legas, da gidan mahaifiyar gwamnan Legas, da sauran muhimman gine-gine da kaddarori musamman na gwamnati.
- Hukumar Gidajen Rediyo da Talabjin ta kasa NBC, ta gargadi gidajen talabijin da rediyo da su dinga yi suna kiyayewa da ka’idojin aikinsu wajen ba da rahoton zanga-zangar da ake yi, don gujewa kara iza wutar tashin hankali da tunzura jama’a.
- Wasu ‘yan bindiga sun kai hari Talatar Mafara ta jihar Zamfara, suka kashe mutum a kalla 22, da satar dabbobi.
- Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Yau ma labarin kwaronabairos ya yi batar dabo. Sawun giwa ya take na rakumi, wato zanga-zanga ta dusashe kwarona.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
Mu wayi gari lafiya.
Af! ‘Yan bindiga sun kashe mutane har ashirin da biyu tashi guda a Talatar Mafara ta jihar Zamfara. Ga wadanda aka kashe a Kidandan ta Giwa da ke jihar Kaduna. Ga na Kagara da ke jihar Neja. Ga na Jibiya da sauran sassan jihar Katsina. Ga na yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna, da kudancin jihar Kaduna, da kidinafas da ke satar na sacewa, da yi wa mata da ‘yan mata fyade, da cinikin mutum har da mata masu shayarwa da masu juna biyu. Su… Af! Bakina da goro. Af! Ga wani can ya ce Guibi ba a tauna goro da asubah sai asuwaki.
Na yi nan.
Za a iya leka rubutun yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.