Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Talata, uku ga watan Rabi’ul Auwal, shekrarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin ga watan Oktoba, na shekarar 2020.
- Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna , sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Akwai sabbin harbuwa da kwarona 118 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 51
Ribas 26
Imo 12
Oshun 8
Filato 6
Abuja 5
Kaduna 4
Ogun 3
Edo 2
Neja 1
Jimillar da suka harbu 61,558
Jimillar da suka warke 56.697
Jimillar da ke jinya 3,736
Jimillar da suka riga ni gidan gaskiya 1,125
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta hannun ministan matasa, ya nemi wadanda ke ci gaba da zanga-zangar #ENDSARS su yi cikin lumana babu tashin hankali ko barin wasu zauna-gari-banza su labe da su, su ta da zaune tsaye.
- Masu zanga-zangar #ENDSARS sun ta da kura a jihar Kano saboda zargin ‘yan sanda sun kashe musu wani, su kuma ‘yan sanda suka musunta.
- Masu zanga-zangar #ENDSARS a jihar Edo sun sa gwamnatin jihar ta sa dokar hana walwala ta sa’a 24 har sai yadda hali ya yi saboda banka wa ofisoshin ‘yan sanda uku wuta, da sanya ‘yan gidan yari tserewa.
- An girke sojoji a wasu yankuna na Abuja don tabbatar da doka, sai da kungiyoyin al’uma sun yi kashedin idan wani soja ya harbi wani daga cikin masu zanga-zangar #ENDSARS ba za su yarda ba. Jiya da yamma an kashe mutum biyu a tsakanin masu zanga-zangar da suka gwabza ya su-ya su.
- Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da nata kwamitin bincike na shari’a na wadanda ‘yan sanda suka zalunta, da ba shi wata shida ya kammala aikin da aka sa shi.
- Ana sa ran daliban kwalejin foliteknik ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic, su soma komawa makaranta ranar biyu ga watan gobe. Su kuwa daliban jami’ar jihar Kaduna jiya suka soma jarabawa.
- Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamatin tarayya, na ci gaba da korafin, shekara daya da wata takwas suna suna dakon ariyas na sabon albashi.
Mu wayi gari lafiya.
Af!
Jiya al’umar Kinkinau na ta korafin an kawo wa kowanne gida ko shago takardar a je a biya kudin zama a duhu na watan Satumba, naira dubu talatin, wasu naira dubu ashirin da tara da wasu kwabbai ko sulalla a sama. Af! Kudin wutar da ba su sha ba, ba kudin zama a duhu ba. Ka ga kullum ko in ce kowanne yini sai ka biya naira dubu daya kudin wuta, ko ka sha ko ba ka sha ba. Nawa ne ma albashi mafi karanci wato MINIMUM WAGE a Nijeriya? In ka cire naira dubu talatin kudin wuta a wata saura nawa?
Na yi nan.
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.