Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Litinin, biyu ga watan Rabi’ul Auwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha tara ga watan Oktoba, na shekarar 2020.

  1. Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawal da na Majalisar Wakilai Gbajabiamila, sun gana da Shugaban Kasa Muhamadu Buhari a kan masu zanga-zangar #ENDSARS kuma bayan sun gama ganawar Ahnad da Femi sun yi kira ga masu zanga-zangar su yi hakuri su tsahirta su daina zanga-zangar haka nan don baiwa gwamnati damar aiwatar da abubuwan da suka bukata kuma gwamnati ta amince. Sai dai Ahmad Lawal da Femi Gbajabiamila sun mance da masu zanga-zanga na Arewa ciki har da Aisha Buhari da ke bukatar a kawo tsaro a Arewa.
  2. A yau za a fara horas da dakarun ‘yan sanda na musamman da suka maye gurbin SARS.
  3. Kugiyar ma’aikatan manfetur da gas ta kasa NUPENG ta ce babu gaskiya a labarun da wasu suka yada cewa za ta dakatar da aikace-aikacenta saboda masu zanga-zangar #ENDSARS.
  4. An daga jarabawar NECO saboda zanga-zangar #ENDSARS da ake ci gaba da yi.
  5. Yau kaf din ma’aikatan kwalejin foliteknik ta Kaduna Kaduna Polytechnic za su koma aiki bayan hutun kwarona.
  6. Yau makarantun jihar Kaduna za su koma bayan hutun kwarona.
  7. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 133 a jihohi da alkaluma 133 kamar haka:

Legas 90
Ribas 19
Abuja 8
Kaduna 8
Oyo 6
Ondo 3
Katsina 2
Nasarawa 2
Filato 1

Jimillar da suka harbu 61,440
Jimillar da suka warke 56,611
Jimillar da ke jinya 3,704
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,125

  1. Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata takwas suna dakon ariyas na sabon albashi.
  2. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  3. Ga wadanda ke iya ganin hoton da ke biye da wannan rubutu na yau, Ibrahima Yakubu ne na rediyon Jamus Dw ke hira da ni jiya a fadata da ke Kaduna.

Mu wayi gari lafiya.

Af!

A daya daga cikin rubutuna na makon jiya na jero lambobin yabo da aka ba ni, da wadanda suka ba ni ciki har da shahararriyar makarantar nan ta Kamtos International Schools da ke Kinkinau a nan Kaduna. Da yake Daraktan makarantar ya ga wancan rubutun nawa, sai na tsinci jiya ya yi wannan tsokaci a dandalina na wasaf na Ishaq Guibi kamar haka:

Assalamu alaikum warahmatullah.
TSOKACI AKAN GABA MAI HARAFIN “I”

KAMTOS INT’L SCH KADUNA, wannan makaranta dake kinkinau no.8 Ahmadu Chanchangi road. Ta amfana kuma tana cikin amfana da gudun mawar da Dr. Is’haq Idris Guibi ke bayarwa ga al’umma ta hanyar ilmantar dasu akan abubuwan dake faruwa a fadin najeriya da wajenta.
Kasurgumin malamin makarantane kuma jibgegen ma’aikancin jarida (Dan jarida) mai fafutukar ganin talaka yasamu sa’ida a rayuwarsa. Wannan Kalmar yabo dayasamu daga wannan makaran nada nasaba da namijin kokarisa da kwamitin wannan biki na shekarar ya gani kuma ya zakulo shi.
Idan da iyaye dake da yara a makarantu sakandire da furamari zasu rika biybiyar karatun yaransu da kuma ziyartar makarantun tare da bada shawarwari da cikakken iko wa malaman makaranta akan yaransu da tarbiyyar yaranmu ta inganta tare da iliminsu.
Daga qarshe ina fatan Allah yayi mana albarka kuma yasa muyi karshe mai kyau amin.
Aliyu Ibrahim Safana
Director,
Kamtos int’l Sch. Kaduna

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.
Yanzun karfe hudu daidai na asubah.

Labarai Makamanta

Leave a Reply