Assalamu alaikum barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, ashirin da biyar ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha bakwai ga watan Yuli na 2020.
- Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a gudanar da cikakken binciken hukumar raya yankin Neja Delta NDDC.
- Magu bai samu hallara ga kwaban kwamitin da ke masa tambayoyi don kare kansa a jiya ba, inda wata majiya ke cewa yana kimtsawa ne.
- Kungiyoyin kwadago na NLC da ULC sun hade wuri guda a yanzun sun dunkule sun zama NLC.
- PDP ta bukaci a hanzartar gurfanar da Magu a gaban kotu.
- Majalisar Dattawa ta yi wa kudirin dokar yin kwalejin ilmi ta gwamnatin tarayya FCE a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna da Sanata Uba Sani ya gabatar karatu na uku.
- Ma’aikatan kwalejojin Foliteknik da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata uku ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
- Ana ci gaba da ba wadanda suka ba shekaru sittin baya a duniya shawarar su dinga natsuwa waje daya don su ne suka fi kasadar harbuwa da kwarona cikin sauki.
- Jiya da daddare kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwarona su 595 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 156
Ondo 95
Ribas 53
Abiya 43
Oyo 38
Inugu 29
Edo 24
Abuja 23
Kaduna 20
Akwai Ibom 17
Anambara 17
Oshun 17
Ogun 14
Kano 14
Imo 11
Delta 6
Ekiti 5
Gwambe 4
Filato 4
Kuros Ribas 2
Adamawa 1
Bauci 1
Jigawa 1
Yobe 1
Jimillar wadanda suka harbu 34,854
Jimillar wadanda suka warke 14,292
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 769
Wadanda ke jinya 19,793
*Kaduna 20, Kano 13 !
- A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito da safiyar nan don lekawa shafukana da ke dauke da labarun da na rubuta daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis. Sai kuma Taskar Guibi da ke Dutsen Kura Communication Limited DCL Hausa da ke dauke da rubutun labarun nawa na kullum, sai jaridar Muryar ‘Yanci ta rediyo da talabijin na Libati/Liberty da ke buga labarun nawa kullum a matsayin sharhin bayan labaru, sai jaridar Kainuwa, da dandali da shafuka, da daidaikun jama’a da kungiyoyi da ke tura labarun da nake rubutawa a kullum, duk ina godiya.
Mu yi juma’a lafiya.
Af! Sakona ya kai ga gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai na cewa tsaro ba shi da lafiya a jihar Kaduna kuma alhaki na kansa kuwa?
Ga Taskar inda za a iya shiga Taskar Guibi :
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.