Sauya Takardun Naira: Mun Gano Gwamnoni Masu Kuruciyar Bera – EFCC

Shugaban hukumar hana cin hanci da rashawa a Najeriya, Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa, adadin gwamnonin da hukumarsa ke sa ido a kansu bisa zargin tara kudin haram ya karu.

Bawa ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, dangane da irin nasarorin da hukumar tashi ta samu.

Bawa ya ki bayyana adadin gwamnonin ko sunayensu, inda yace ba ya son a yi masa mummunar fahimta ko a sauya mishi magana.

An ce gwamnonin suna kokarin fara fitar da kudaden tare da tabbatar da sun sauya su cikin sauki biyo bayan kudurin babban bankin Najeriya (CBN) na sake fasalin wasu kudaden kasar nan.

Shugaban na EFCC ya kuma yabawa CBN bisa kawo wannan tunani na sake fasalin kudi, inda yace hakan zai taimakawa hukumar wajen yaki da almundahana a kasar. A cewarsa, kudaden da suka bar hannun CBN suke yawo a hannun jama’a, musamman wadanda aka boye suna taimawa wajen karuwar laifukan da suka shafi rashawa a Najeriya.

Daga karshe ya shawarci ‘yan siyasa da su yi taka tsan-tsan wajen yin kamfen da kudaden da haram domin illar dake tattare da hakan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply