Sauya Shekar Gwamna Matawalle Bai Saba Doka Ba – Kotu

Rahotannin daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa Babban Kotun jihar ta yi watsi da karar da aka kai gabanta da ake kalubalantar ci gaba da zaman Gwamna Bello Matawalle gwamnan jihar bayan canja sheka da yayi.

Alkalin kotun ya bayyana cewa duk da cewa wannan ba a hurumin sa ya ke, ya ce babu inda dokar kasa tace don wani ya canja sheka shikenan sai kuma ya sauka daga kujerar da yake akai.

” Dokokin jam’iyyun kasar nan ba su hana sauya sheka ba, haka kuma dokar kasa bai hana ba. Saboda haka Matawalle bai aikata laifi ba sauya jam’iyyar da yayi.

A karshe sai alkali Bappa Aliyu ya umarci wadanda suka kai kara su biya gwamna Matawalle, minista Malami, da jam’iyyar APC naira miliyan 1 kowannen su saboda bata musu lokaci da masu kara suka yi a kotu.

Idan ba a manta ba gwamna Matawalle ya tsinci dame a kale ne bayan kotun koli ta soke zabukan jam’iyyar APC kaf ta baiwa PDP duka kujerun jihar.

Kotu ta ce jam’iyyar APC bata yi zabukan fidda gwani ba tun farko.

Labarai Makamanta

Leave a Reply