Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa nan bada jimawa ba abubuwa za su fara sauyawa zuwa farin ciki a Najeriya. Shugaban ƙasar ya ba da wannan tabbaci ne yayin da ƴan Najeriya ke fama da wahalhalun tsadar rayuwa sakamakon wasu sauye-sauyen gwamnati, The Cable ta rahoto.
Bola Tinubu ya ce yana sane da cewa ‘yan Najeriya na korafi kan yunwa, inda ya kara da cewa gwamnatinsa ta fito da kayan jin kai domin a magance illolin yunwa.
Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa a shirye take ta aiwatar da sabon mafi karancin albashi, Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, yayin bikin kaddamar da shirin mata na Najeriya.
Ya ce: “Gwamnatina zata tafi da mata kuma wannan na ɗaya daga cikin tsare-tsare na, ina alfaharin tsayawa a gabanku yau kuma na gaya muku cewa goben matan Najeriya za ta yi kyau. “A matsayinmu na gwamnati aikinmu ne mu ba da fifiko ga ’yan ƙasa masu rauni waɗanda sune mata da kananan yara.”
Da yake tsokaci kan halin yunwa da ake ciki, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa zata yi duk mai yiwuwa ta hanyar samar da tallafi domin al’umma su ci su ƙoshi.
“A yau ana nuna damuwa kan yunwa, zamu fito da kayan abinci domin kawar da duk wata illa ta yunwa, abubuwa sun yi wahala amma ba zamu zauna dindindin a haka ba. “Nan bada daɗewa ba abubuwa za su fara canzawa saboda zamu fito da ƙarin abinci ga al’umma, sannan a shirye muke mu aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi.”