Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hafsan rundunar sojin sama, Air Marshall Isiaka Amao, ya tabbatar wa yan majalisar dattawa cewa lokaci kaɗan ya rage ayyukan ta’addanci da yan bindiga ya zama tarihi a Najeriya.
Amao ya bada wannan tabbacin ne kwanaki uku kacal bayan mayakan ISWAP sun kashe Janar na sojojin ƙasa a Askira Uba, jihar Borno. Majalisar dattijai, ta hannun kwamitin sojojin sama, sun bukaci rundunar sojin su ƙara ƙaimi a yakin da suke domin tabbatar da zaman lafiya a wuraren da lamarin ya shafa.
Hafsan sojin saman ya yi wannan furucin ne yayin da yake kare kasafin kuɗin shekarar 2022 a gaban kwamitin majalisar dattijai ranar Talata.
Yace yan ta’adda na kowane kungiya, Boko Haram ko ISWAP, suna shan luguden wuta ta ko ina kuma ba kakkautawa, wanda hakan ke tilasta musu aje makamai da mika wuya.
“Bisa nauyin da aka dora wa rundunar sojin sama da na ƙasa, martabar Najeriya na nan yadda aka santa kuma an kare ta daga yan ta’adda da yan bindiga, waɗanda ba da jimawa ba zasu zama tarihi.”
Amao ya kara da cewa kasafin kudin da gwamnati ke ingiza wa rundunar sojin sama, tana amfani da su ne wurin cigaba da yaƙar yan ta’adda a kowane lungu na Najeriya ba kakkautawa.
Hakazalika yace rundunar na amfani da kuɗaɗen wajen kara kula da walwala da jin dadin jami’an soji. “A dai-dai wannan lokaci da muke fuskantar ƙalubale, wajibi mu sa basira da tattali wajen tafiyar da kasafin kudin da muka samu.”