Saura ?iris Ta’addanci Ya Zama Tarihi A Najeriya – ?ungiyar Gwamnoni

Shugaban kungiyar Gwamnonin Nijeriya, kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Mista Kayode Fayemi ya ce sakamakon aiki tukuru da jajircewa da kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, an kusa shawo kan matsalar rashin tsaron da ta addabi sassan Nijeriya nan gaba kadan.

Mista Kayode Fayemi ya bayyana haka, a Katsina lokacin da kungiyar ta kawo ziyarar jaje da nuna goyan baya ga yunkurin gwamna Masari na kawo karshen matsalar yan bindiga da suka addabi jihar Katsina da sace-sacen mutane da kisan wadanda ba su ji, ba su gani ba.

Shugaban kungiyar Gwamnonin Nijeriya, ya kara da cewa Muna da yakinin gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, yana kokari matuka wajen kawo karshe wannan matsalar, kuma yana aiki kafada-da-kafada da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Mun yaba da irin kokarin kubutar da yara dari ukku da arba’in da hudu da aka sace a makarantar sakandire ta Kankara a dajin jihar Zamfara.

Mun zo jihar Katsina ne, domin Jajantawa Al’ummar Jihar Katsina dangane da sace wadannan dalibai da gwamnatin jihar Katsina da kuma ba su tabbacin, nan da lokaci kadan za’a kawo karshen ta’addanci yan bindiga a jihar Katsina da kuma kasa baki daya da yardar Allah.

Cikin gwamnonin da suka samu ziyartar jihar Katsina, a karkashin kungiyar Gwamnonin akwai Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu da kuma Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar

Related posts

Leave a Comment