Saudiyya Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Da Boko Haram Ta Yi Wa Manoma

Ƙasar Saudiyya ta nuna alhininta a kan kisan manoman shinkafa da ‘Yan ta’addan Boko Haram suka yi wa Manoman Shinkafa a ƙauyen Zabarmari dake ƙaramar Hukumar Jere Jihar Borno.

Saudiyya ta wallafa wannan sakon a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ta nuna alhininta a kan yadda maharan suke kai wa fararen hula wadanda ba su ji ba, ba su gani ba farmaki da kisa.

“Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda aka kashe, da mutanen jihar, gwamnati da al’ummar Najeriya gaba daya.”

Kasar Bahrain ta mika kwatankwacin ta’aziyyar nan ga Najeriya, inda tace tana fatan ganin karshen ta’addanci a Najeriya nan kusa.

Kisan Zabarmari dai na cigaba da ɗaukar hankalin duniya, inda jama’a da dama suka nuna damuwa da kiran Gwamnatin Najeriya da yin gaggawar ɗaukar matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar ayyukan ta’addanci wanda ya addabi ƙasar musanman yankin Arewacin Najeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply